Yan bindiga
Rundunar sojin Najeriya ta kama wasu mutane da suke kera bindigogi suna rabawa 'yan ta'adda a jihohin Arewa ta Yamma. An kama su da bindigogi biyar.
Rundunar yan sanda ta bayyana cewa ta tura dakaru zuwa yankin bayan samun labarin kashe almajirai da garkuwa da wasu yan gida daya a jihar Bauchi.
'Yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a cibiyar NIPSS da ke jihar Plateau. Jami'an tsaro sun fito an yi gumurzu wanda ya kai ga dakile harin.
Mazauna kauyen Dansarai a Katsina sun yi artabu da ‘yan bindiga, inda aka kashe mutane hudu tare da fatattakar maharan. An ce 'yan bindiga sun tsere da suka ji wuta.
'Yan bindiga sun yi awon gaba da wani fasto da ke shugabantar wata coci a jihar Benue. Hatsabiban sun kuma hada har da wasu mambobin cocinsa yayin harin.
‘Yan bindiga sun kashe jami’an ‘yan sanda biyu tare da raunata wani a Rivers a wani shingen bincike, yayin da rundunar ta fara bincike don kamo maharan.
Dan Majalisar Wakilai na jam'iyyar APC daga jihar Plateau, Yusuf Gagdi, ya nuna alamar tambaya ga yan adawa kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a Najeriya.
Bincike ya tabbatar da cewa babu wata hujja ingantacciya da ke tabbatar da cewa yaron da ya bayyana a wani hoto mai yaduwa shi ne ya sace Janar Rabe Abubakar.
Wani saƙo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta ya yi ikirarin cewa an kama sarakunan Alabe da Babanla da matansu a Kwara bisa zargin garkuwa da mutane.
Yan bindiga
Samu kari