Dalla Dalla: Yadda Za a Kai Korafi ga EFCC kan Zargin Damfara, Badakala

Dalla Dalla: Yadda Za a Kai Korafi ga EFCC kan Zargin Damfara, Badakala

  • Hukumar yaki da cin hanci ta EFCC ta bayyana yadda ake shigar da koke kan zargin damfara da badakala ta shafinta
  • Masu kai ƙorafi za su cika bayanan kansu, na wanda ake zargi, da cikakken bayanin lamarin, tare da adadin kuɗi da wurin da abin ya faru
  • EFCC ta ce ana iya ɗora takardun shaida ko hotuna masu girman kasa da 'megabite' 10 ba, sannan mai ƙorafi ya tabbatar da ba da bayanansa gaskiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC) ta kawo tsarin mika korafi daga alumma.

EFCC ta bayyana yadda jama'a za su iya shigar da koke kan zargin damfara da sauran laifukan kuɗi ta hanyar shafinta na intanet.

EFCC ta fadi yadda za a kai mata korafi
Shugaban hukumar EFCC a Najeriya, Ola Olukoyede. Hoto: Economic and Financial Crimes Commission.
Source: Facebook

A cewar hukumar a shafinta na Facebook, duk wanda zai shigar da ƙorafi dole ne ya bayar da sahihan bayanai, domin shigar da ƙorafin ƙarya laifi ne a ƙarƙashin doka.

Kara karanta wannan

Kotu ta ci tarar dan takarar gwamna a ADC miliyoyi kan fastocin siyasa a Adamawa

Gargadin da hukumar EFCC ta yi

EFCC ta yi gargadin cewa Sashe na 64(3) na Dokar 'Corrupt Practices and Other Related Offences Act' ta shekarar 2000 ya tanadi hukuncin ɗaurin shekaru har 10 ko tara da ba ta wuce Naira 100,000 ga duk wanda ya shigar da ƙorafin ƙarya.

Domin shigar da koke, mai ƙorafi zai cika fom na intanet da bayanansa kamar suna na farko, na tsakiya idan akwai, suna na ƙarshe, lambar NIN, nau'in ƙorafi, jinsi, lambar waya, adireshin imel, ƙasa, jiha, ƙaramar hukuma da adireshin zama.

Haka kuma, dole ne a cika bayanan da suka shafi shari'ar, ciki har da taken ƙorafin, sunan wanda ake zargi, inda yake, sunan mai ƙorafi, wurin da ake zargin laifin ya faru, adadin kuɗin da abin ya shafa da kuma nau'in kuɗin.

A sashen bayanin ƙorafi, ana buƙatar mai ƙorafi ya rubuta cikakken bayani kan abin da ya faru domin bai wa EFCC damar fahimtar lamarin yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

'Kar mu ji, kar mu gani': Atiku ya gargadi gwamnati game da Obi, El Rufa'i

EFCC ta gargadi mutane kan tura korafin cin hanci gare ta
Jami'an hukumar yaki da cin hanci a bakin aiki. Hoto: Economic and Financial Crimes Commission.
Source: Twitter

Tsarin yadda EFCC ke bukatar korafi

Hukumar ta kuma ba da damar ɗora takardun shaida ko hotuna domin tallafa wa ƙorafin, kodayake yin hakan ba wajibi ba ne ga masu shigar da koke.

EFCC ta bayyana cewa takardun da ake karɓa sun haɗa da fayel mai tsarin PDF da hotuna, kuma girman kowane fayel bai kamata ya wuce 'megabite' 10 ba.

Kafin a aika da ƙorafi, mai shigarwa dole ne ya kammala tantancewar tsaro sannan ya tabbatar cewa ya karanta kuma ya fahimci gargadin da ya shafi ƙorafin ƙarya.

Hukumar ta jaddada cewa bayar da cikakkun bayanai masu inganci da gaskiya zai taimaka mata wajen bincike da sarrafa koke cikin sauri da inganci.

An buɗe hanyar shigar da ƙorafi ta shafin intanet na hukumar EFCC, inda masu buƙata za su iya aika koke tare da bin duk matakan da hukumar ta tanada.

Yan Yahoo sun yashe asusun alkali

Kara karanta wannan

Yadda shugaban ma'aikatar bogi ya yaudari mataimakin shugaban majalisar wakilai

Mun ba ku labarin cewa masu aikata damfarar intanet wanda aka fi sani da 'yan Yahoo sun taba yashe kudaden wata alkalin kotu a tsakar dare.

Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana yadda lamarin ya kasance, yayin ya ke sukar ayyukan 'yan Yahoo.

Ola Olukoyede ya nuna muhimmancin da ke akwai na yin hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki yaki da matsalar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.