Wuya Ta Yi Wuya: Sarakuna 30 a Najeriya Sun Ji Tsoro, Sun Tsere daga Garuruwansu
- Aƙalla sarakunan gargajiya 30 a Kwara ne tsere daga fadarsu sakamakon yawaitar garkuwa da mutane, kisan gilla, da hare-haren ’yan bindiga
- Bincike ya nuna cewa sarakunan suna neman mafaka a manyan birane kamar Ilorin, Offa, da Legas, lamarin da ya haifar da giɓin shugabanci a yankunan
- Omugo da Oreke na daga cikin garuruwan da suka kusan zama kufai, inda sarakunansu ba su iya zama a fada sakamakon tsoron harin ’yan ta’adda
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kwara – Wani bincike na musamman da aka gudanar ya bayyana halin fargaba da gudun hijira da suka mamaye yankun karkara na jihar Kwara.
Rahoton ya nuna yadda sarakunan gargajiya fiye da 30 suka tsere daga fadarsu domin tsira da rayukansu.

Source: Original
Sarakuna 30 sun tsere daga fadarsu
Waɗannan sarakunan, waɗanda galibinsu sun fito ne daga yankin kudancin jihar, yanzu haka suna gudun hijira a birane daban-daban, kamar yadda binciken na jaridar Punch ya nuna.
Garuruwan da sarakuna suka tafi gudun hijira sun hada da Ilorin, Osogbo da kuma Legas, sakamakon barazanar ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane.
Garuruwan da abin ya shafa sun haɗa da Omugo, Afin, Oreke, Alabe, da sauran yankunan da ke kusa da su.
Mazauna waɗannan yankuna sun bayyana cewa sarakunan ba sa iya zama a garuruwansu domin su ne babban burin masu garkuwa.
Wani mazaunin Omugo, Wale Olasunkanmi, ya bayyana cewa sarkinsu yanzu haka ba ya zama a garin sai dai idan akwai wani taro na musamman da ba za a iya fashi ba, inda yake dawowa na ɗan lokaci sannan ya sake guduwa birni kafin dare ya yi.
Hare-haren 'yan bindiga sun tsorata sarakuna
Rashin sarakunan a yankunansu ya haifar da babban cikas wajen yanke shawara da kuma daidaita ayyukan tsaro na sa-kai a yankunan.
A garin Oreke, lamarin ya yi muni tun watan Yunin 2025 bayan an kashe jami’an sanda biyu a wani wurin hakar ma’adinai, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Rashin imani: Bam ya tashi da mutane da yawa, yan ta'adda sun bi su da harbi a Borno
Wani ma’aikacin fada, Samuel Afolayan, ya bayyana cewa:
"Fadar sarki a yanzu haka wayam take, babu kowa. Sarkin ba ya nan, kuma mazauna garin ma sun tsere. Tun watan Yunin bara ban sake sa ƙafa a garin namu ba."
Wannan ya sa yankin ya zama tamkar kufai, inda yanzu babu harkokin kasuwanci ko na noma da ke gudana yadda ya kamata saboda fargabar harin bazata.

Source: Facebook
An hana sarki komawa fada bayan sace shi
Daga cikin sarakunan da suka fuskanci mafi munin yanayi har da Oniwo na Afin, Oba Simeon Olaonipekun. An sace sarkin tare da ɗansa a daren jajibirin sabuwar shekara ta 2026, cewar rahoton The Guardian.
Ko da yake ya sami ’yanci bayan an biya kuɗin fansa fiye da naira miliyan 30, sarkin ya kasa komawa fada sakamakon raunin da ya ji da kuma tsoron abin da ka iya sake faruwa da shi a can karkarar.
Majiyoyi daga fadar sarkin sun tabbatar da cewa likitoci sun shawarci sarkin da ya zauna a birni domin samun kulawa da kuma hutu sakamakon shekarunsa da kuma azabtarwa da ya gani a hannun masu garkuwa.

Kara karanta wannan
Hormuz: Matakin Amurka da Iran ya ta'azzara farashin fetur a duniya, ganga ta haura $100
'Yan bindiga sun kashe sarki da iyalansa
A wani labari, mun ruwaito cewa, tsagerun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci tare kashe wani basarake a jihar Benue.
'Yan bindigan sun kashe mutane biyar, ciki har da wani basarake, matarsa, ɗansa da wasu mazauna yankin su biyu a rukunin gidajen Olegabulu da ke ƙaramar hukumar Agatu a Benue.
Shugaban ƙaramar hukumar Agatu, Melvin Ejeh, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai bayyana cewa mutane biyar ne aka kashe yayin da mutum ɗaya ya ji rauni.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
