Yan Bindiga Sun Yi Ta’asa, Sun Hallaka Ministan Tsaron Mali yayin Hari a Gidansa

Yan Bindiga Sun Yi Ta’asa, Sun Hallaka Ministan Tsaron Mali yayin Hari a Gidansa

  • Ministan tsaron Mali, Janar Sadio Camara, ya mutu bayan hare-haren hadin gwiwa kan sansanonin soji a sassa daban-daban
  • Maharan da suka hada da kungiyoyin da ke da alaka da al-Qaeda da kuma mayaƙan Tuareg sun kai harin kunar bakin wake a gidansa da ke Kati
  • Ana kallon mutuwar Camara a matsayin babbar illa ga rundunar sojin Mali, yayin da hare-haren ke ci gaba a wurare da dama

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bamako, Mali - Ministan tsaron Mali, Janar Sadio Camara, ya rasu sakamakon hare-haren hadin gwiwa da aka kai kan wuraren soji a sassa daban-daban a kasar.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne bayan yan bindiga sun kai hari a gidansa da ke garin Kati, wanda ke kusa da Bamako a ranar Asabar 25 ga watan Afrilun 2026.

Kara karanta wannan

Cole Allen: Abubuwan mamaki game da matashin da ya kai hari kan su Donald Trump

Yan bindiga sun kashe ministan tsaron Mali
Ministan tsaron kasar Mali, Sadio Camara yayin taro a Bamako. Hoto: FANNY NOARO-KABRE/AFP.
Source: Getty Images

Yan bindiga sun kashe ministan tsaron Mali

An bayyana cewa wasu kungiyoyi masu alaka da al-Qaeda tare da mayaƙan Tuareg ne suka kai harin, inda suka yi amfani da motar kunar bakin wake wajen kai farmakin, cewar Al Jazeera.

Kati na daga cikin wuraren da ake ganin suna da tsaro sosai a Mali, amma duk da haka maharan sun samu damar kai wannan hari mai girma.

Masana sun bayyana Camara a matsayin daya daga cikin manyan jiga-jigan gwamnatin mulkin soja, wanda aka kafa bayan juyin mulki da aka yi a shekarun 2020 da 2021.

Rahotanni sun ce mutuwarsa babbar illa ce ga rundunar sojin Mali, musamman a daidai lokacin da ake fama da hare-haren kungiyoyin masu dauke da makamai.

Har yanzu ana ci gaba da jin karar harbe-harbe da fashe-fashe a wasu yankuna kamar Kidal da Gao, alamar cewa rikicin bai lafa ba, kamar yadda Reuters ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An kama mai taimaka wa yan bindiga su samu kudi a Sakkwato, ya fara bayani

An kashe ministan tsaro a Mali
Shugaban kasar Mali, Assimi Goita yana jawabi a taro. Hoto: MALIK KONATE.
Source: Getty Images

Fargabar da ake yi a Mali

Masana tsaro sun yi gargadin cewa ana iya samun karin fada kan iko da muhimman wurare a cikin kwanaki masu zuwa.

An kuma bayyana cewa kungiyoyin da a baya suke yaki da juna sun hada kai domin kai hare-hare kan gwamnatin Mali.

Kungiyar Tarayyar Afirka da sauran kungiyoyin kasa da kasa sun yi Allah wadai da wadannan hare-hare, suna kira da a dauki matakan gaggawa don dawo da zaman lafiya.

Wani ɗan uwa, da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ministan da aƙalla mutum uku daga cikin iyalansa sun mutu sakamakon bam ɗin mota da wata ƙungiya mai alaƙa da kungiyar Al Qaeda ta dasa.

Mali, Burkina Faso sun yi barazana ga Najeriya

Mun ba ku labarin cewa rahotanni sun nuna cewa kungiyar AES ta ba da umarni cewa a harbo duk wani jirgin da ya keta sararin samaniyar mambobinta.

Kara karanta wannan

Iran ta kafa tarihi a duniya bayan shiga kwana na 57 a yakinta da Isra'ila

Umarnin ya biyo bayan zargin cewa jirgin saman sojojin Najeriya ya shiga sararin samaniyar Burkina Faso ba tare da izini ba.

Shugaban kasar Mali, Asimi Goita ya ce shiga yankinsu ba tare da izini ba rashin mutuntawa ne ga dokokin ƙasa da ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.