'Yan Bindiga Sun Zo da Sabon Salon Ta'addanci, Sun Kashe Basarake da Iyalansa
- 'Yan bindiga sun kai harin ta'addanci kan mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a jihar Benue a tsakiyar Najeriya
- Tsagerun 'yan bindigan sun saje da mutane kafin daga bisani su kutsa fadar basarake tare da hallaka shi da iyalansa
- 'Yan bindigan sun kuma kashe karin wasu mutane a harin wanda suka kai a karamar hukumar Agatu ta jihar Benue
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Benue - Tsagerun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci tare kashe wani basarake a jihar Benue.
'Yan bindigan sun kashe mutane biyar, ciki har da wani basarake, matarsa, ɗansa da wasu mazauna yankin su biyu a rukunin gidajen Olegabulu da ke ƙaramar hukumar Agatu a jihar Benue.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa mazauna yankin sun bayyana cewa harin ya faru ne a daren ranar Alhamis, 23 ga watan Afirilun 2026.
'Yan bindiga sun yi ta'asa a Benue
Maharan waɗanda suka zo kan babura biyu, sun far wa gidan basaraken ne tare da buɗe masa wuta shi da iyalansa.
Wani mazaunin yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce mahara huɗu ne suka gudanar da farmakin.
A cewarsa, sun shigo yankin ne ba tare da nuna wata alamar zargi ba, sannan suka nufi fadar kai tsaye inda suka harbe basaraken, matarsa da ɗansa har lahira.
Ya ƙara da cewa daga baya maharan sun nufi wani gida na kusa, inda suka kashe wasu mazauna yankin su biyu kafin su tsere daga wurin.
'Yan bindiga sun yaudari mutane
Wasu shaidu sun ce maharan sun fara ne ta hanyar haɗewa da mutanen yankin, inda suke gaisawa da su cikin yaren yankin, jaridar The Punch ta kawo rahoton.
“Maharan ba Fulani ba ne. Lokacin da suka zo, sun tattauna cikin walwala da mutane da yarenmu, don haka babu wanda ya zarge su da cewa makiya ne."

Kara karanta wannan
Malami ya umarci mabiyansa a Najeriya su ba 'yan bindiga lambar wayarsa idan aka sace su
“Amma suna shiga gidan basaraken, sai suka buɗe wuta, mutane kuma suka fara gudu don tsira."
“Sun kwashe kusan mintuna 20 suna aikata danyen aikin. Bayan sun kai hari gidan basaraken, sai suka koma wani gida na kusa suka kashe wasu mutane biyu. Mutum ɗaya ya ji rauni kafin su tsere."
- Wata majiya
Me hukumomi suka ce kan lamarin?
Shugaban ƙaramar hukumar Agatu, Melvin Ejeh, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai bayyana cewa mutane biyar ne aka kashe yayin da mutum ɗaya ya ji rauni.
“Gaskiya ne lamarin ya faru. An kashe mutane biyar sannan mutum ɗaya ya ji rauni a lokacin harin."
- Melvin Ejeh

Source: Original
Melvin Ejeh ya ƙara da cewa jami’an tsaro, ciki har da ‘yan sanda, sun ziyarci wurin da abin ya faru.
Lokacin da aka tuntuɓi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Benue, DSP Udeme Edet, ta ce har yanzu ba ta samu cikakken bayani kan lamarin ba.
'Yan ta'adda sun sace likita
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun kai farmaki a wani asibitin kudi da ke jihar Neja, inda suka yi awon gaba da likita.
'Yan ta'addan sun yi garkuwa da wani likita mai suna Anthony Enahoro, a gundumar Wawa da ke ƙaramar hukumar Borgu a jihar Neja.
Mutanen yankin suna zargin cewa 'yan ta'addan sun yi awon gaba da likitan ne domin ya ba da magani ga mayakan da suka ji rauni ko kuma waɗanda ba su da lafiya.
Asali: Legit.ng

