"Sun Nemi N300m: 'Yan Bindiga Sun Sace 'Yan Uwan Gwamna Dauda Lawal

"Sun Nemi N300m: 'Yan Bindiga Sun Sace 'Yan Uwan Gwamna Dauda Lawal

  • Gwamna Dauda Lawal ya ce ya ƙi biyan Naira miliyan 300 lokacin da aka sace 'yan'uwansa a 2019
  • Ya bayyana cewa masu garkuwar sun saki 'yan'uwansa bayan watanni uku ba tare da sun karɓi kuɗin fansa ba
  • Gwamna Dauda Lawal ya sake jaddada buƙatar kafa 'yan sandan jihohi domin gwamnoni su samu ikon kula da tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa ya ƙi biyan Naira miliyan 300 da masu garkuwa da mutane suka buƙata lokacin da suka sace 'yan'uwansa a shekarar 2019.

Gwamna Dauda ya ce ya ɗauki wannan matsaya ne saboda ya yi amanna cewa biyan kuɗin fansa yana ƙara ƙarfafa masu aikata laifuka su ci gaba da sace mutane domin neman kuɗi.

'Yan bindiga sun sace yan uwan Dauda Lawal
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara Hoto: Sulaiman Bala Idris
Source: Facebook

Abin da Dauda Lawal ya ce kan biyan kuɗin fansa

Kara karanta wannan

Cuta ta barke a sansanin 'yan ta'addan ISWAP, mayaka da dama sun mutu a Borno

Jaridar The Punch ta ce ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a taron ARISE News a Abuja ranar Alhamis, 9 ga watan Yulin 2026.

Gwamna Dauda Lawal ya ce bai amince da yin sulhu da masu garkuwa da mutane ba duk da cewa abin ya shafi iyalansa.

"An sace 'yan'uwana a shekarar 2019, kuma masu garkuwa sun nemi kusan Naira miliyan 300. Na ce ba zan biya ko sisi ba. Idan suna so, su kashe su."

- Gwamna Dauda Lawal

A cewarsa, bayan sun shafe watanni uku a hannun masu garkuwar, daga ƙarshe an saki 'yan'uwansa ba tare da biyan ko kwabo na kuɗin fansa ba.

"Idan muka ci gaba da biyan kuɗin fansa, muna ƙarfafa su ne su ci gaba da sace mutane."

- Gwamna Dauda Lawal

Ya ƙara da cewa idan masu aikata irin waɗannan laifuffuka suka fahimci cewa ba za a biya kuɗin fansa ba, za su sake tunani kafin su sace mutane.

Gwamna Dauda ya sake jaddada matsayarsa

Dauda Lawal ya ce matsayarsa kan batun biyan kuɗin fansa bai canja ba.

Kara karanta wannan

'Kar mu ji, kar mu gani': Atiku ya gargadi gwamnati game da Obi, El Rufa'i

"Ba zan yi sulhu ba, kuma ba zan biya kuɗin fansa ga wani ɗan ta'adda ko mai laifi ba, komai ya faru."

- Gwamna Dauda Lawal

'Yan bindiga sun taba sace yan uwan Dauda Lawal
Gwamna Dauda Lawal na jawabi a wajen taro Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Ya nemi a kafa 'yan sandan jihohi

Gwamnan ya yi waɗannan kalamai ne yayin da yake bayyana goyon bayansa ga kafa 'yan sandan jihohi, rahoton Daily Post ya nuna haka.

Ya ce idan ana son a riƙa ɗora wa gwamnoni alhakin kare rayuka da dukiyoyin al'umma, dole ne a ba su ikon tafiyar da harkokin tsaro a jihohinsu.

Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa ɗaya daga cikin abubuwan da ke damunsa shi ne yadda ake kiransa babban jami'in tsaro na jiha, alhali ba shi da ikon ba jami'an tsaro umarni.

"Ko da yake ana kirana babban jami'in tsaro na jiha, ba ni da ikon jagoranci ko ba wasu jami'an tsaro umarnin abin da ya kamata su yi."

- Gwamna Dauda Lawal

Gwamna Dauda ya amince a fara biyan alawus

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara, ya amince da fara biyan alawus ga masu yin NYSC.

Gwamna Dauda ya ce ya dauki matakin ne domin nuna godiya ga kishin kasa, sadaukarwa da gudunmawar da mambobin NYSC ke bayarwa a fannoni daban-daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng