Yan Bindiga Sun Harbi Malamin Musulunci kuma Tsohon Kwamishina, Yana Kwance a Asibiti
- Wani tsohon kwamishina a Zamfara,m ya tsallake rijiya ta baya bayan wani mummunan harin ƴan bindiga
- An ce Sheikh Abdullahi Maharazu Mafara ya gamu da tsautsayi bayan ‘yan bindiga sun bude masa wuta a hanyar zuwa taron SO
- Lamarin ya faru ne yayin da yake tafiya daga Talata Mafara zuwa Gusau domin halartar taron APC, inda aka yi masa kwanton bauna tare da harbe-harbe
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Wani tsohon kwamishinan harkokin addini a Zamfara, Sheikh Abdullahi Maharazu Mafara, ya gamu da harin ƴan bindiga.
Malamin wanda dan siyasa ne ya tsallake rijiya da baya bayan wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun bude masa wuta.

Source: Twitter
An farmaki tsohon kwamishina a Zamfara
Rahotanni daga shafin Bakatsine sun nuna cewa lamarin ya faru ne ranar Asabar yayin da malamin yake kan hanyarsa daga Talata Mafara zuwa Gusau domin halartar wani taron jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan
Abu ya girma: Martanin Netanyahu kan harin da aka yi yunkurin kashe Trump, matarsa
Sai dai maharan sun yi masa kwanton bauna a hanya inda suka bude wuta sau da dama kan motarsa, lamarin da ya jikkata shi a kafarsa amma bai rasa ransa ba.
Wata majiya daga Sahara Reporters ta tabbatar da harin, inda ta bayyana cewa an nufi harin ne kan malamin wanda ya taba zama shugaban karamar hukuma a baya.
“Ya samu rauni a kafa sakamakon harbin bindiga; an cire harsashin kuma yanzu yana samun kulawa a asibitin koyarwa na Usmanu Danfodiyo.
- In ji sanarwar

Source: Original
Wannan sabon hari ya sake tayar da damuwa kan tabarbarewar tsaro a Zamfara, musamman a manyan hanyoyi da suka zama wuraren yawaitar ‘yan bindiga da garkuwa da mutane.
Masana tsaro sun nuna damuwa kan yadda har manyan mutane ke fuskantar hare-hare, suna tambayar dalilin da yasa hanyoyin Zamfara ke ci gaba da zama marasa tsaro.
Yadda Zamfara ke fama da matsalolin tsaro
Zamfara na fama da matsalar ‘yan bindiga tsawon shekaru, inda kungiyoyin masu laifi ke kai hare-hare kan kauyuka, sace jama’a da kuma kai farmaki ga matafiya ba tare da tsangwama ba.
Ba shi ne karon farko ba da miyagu ke kai farmaki kan yan siyasa a Arewacin Najeriya, lamarin da ke kara sanya tsoro a zukatan mutane duba da cewa manyan kasa ma ba su tsira ba.

Kara karanta wannan
Jami'ai sun kai wa Trump da matarsa dauki bayan ɗan bindiga ya kai hari taron White House
Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto, babu wata sanarwa daga hukumomi ko gwamnati da jam'iyyar APC game da abin da ya faru na takaici a Zamfara.
Yan bindiga sun bude wata kan masoyan Fubara
A baya, mun ba ku labarin cewa wasu ‘yan bindiga sun bude wuta kan matasan da ke taron siyasa a Elele, karamar hukumar Ikwerre, inda ake zargin mutum 14 sun jikkata.
Wani ganau ya ce wani jagoran sa-kai ne ya kai harin, kuma har ya yi barazanar kai farmaki kan magoya bayan Gwamna Siminalayi Fubara.
‘Yan sanda sun cafke mutum daya daga cikin ‘yan bindigar, sun kwace makamin da ya ke hannunsa, suna ci gaba da farautar sauran maharan.
Asali: Legit.ng