An Harbe 'Yan Bindiga har Lahira bayan Gwabza Fada da 'Yan Sanda

An Harbe 'Yan Bindiga har Lahira bayan Gwabza Fada da 'Yan Sanda

  • 'Yan sandan jihar Ogun sun kashe masu garkuwa da mutane 2 da suka yi garkuwa da yariman Okun Owa, Prince Idris Adesulu
  • Jami'an tsaro sun kwace bindiga kirar AK-47 da kaya masu alaka da aikin laifi bayan sun gwabza da 'yan bindigan a yankin Agoro/Imodi
  • Rahoto ya nuna cewa an dawo da Prince Idris Adesulu gida lafiya lafiya a ranar 3 ga Yulin 2026 bayan an yi garkuwa da shi a ranar 30 ga Yuni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ogun - Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Ogun sun hallaka mutane biyu da ake zargi da yin garkuwa da yariman Okun Owa a karamar hukumar Odogbolu.

An yi garkuwa da yariman wanda ake kiransa Prince Idris Adesulu ko Osho a gidansa da ke titin Ogbe a ranar 30 ga Yuni 2026, kusan karfe 7:30 na dare.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya kausasa murya kan 'yan bindiga, ya ce a hada kai a yake su

Taswirar jihar Ogun
Taswirar jihar Ogun a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Daily Trust ta rahoto cewa shaidu sun bayyana cewa 'yan bindigan sun yi wa gidansa kwanton bauna, suka bude wuta, duk da cewa 'yan uwan yariman sun samu damar gudu, sun kama shi da karfi.

Matakin da yan sanda suka dauka

Bayan an sami labarin, kwamishinan 'yan sanda na jihar, CP Bode Ojajuni, ya ba da umarni nan take a tura rundunar yaki da garkuwa da mutane tare da sauran dakarun tsaro wajen.

An tura su ne domin kwato yariman cikin aminci da kuma kama wadanda suka aikata laifin, kamar yadda jami'in hulda da jama'a na 'yan sanda, DSP Oluseyi Babaseyi, ya sanar a wata sanarwa ranar Alhamis.

An harbe 'yan bindiga 2

Rahoton da DPS Babaseyi ya fitar ya tabbatar da cewa an saki yariman ba tare da an cutar da shi ba a ranar 3 ga Yuli 2026.

Bayan an dawo da yariman, jami'an 'yan sanda ba su tsaya sanya be, sun cigaba da kokarin kama wadanda suka yi garkuwa da shi.

Kara karanta wannan

An bankado wurare masu hadari a Abuja, an kama mutum 560 da bindigogi

Ta hanyar bayanai masu inganci, jami'an suka dura yankin Agoro/Imodi inda suka gano mashigar masu garkuwan a wani waje.

Lokacin da 'yan bindigan suka ga jami'an tsaro, suka fara harbi, amma jami'an suka mayar musu da martani da karfi, wanda ya kai ga hallaka mutane biyu daga cikin 'yan bindigar da raunata wasu.

Shugaban 'yan sandan Najeriya
Sufeton 'yan sandan Najeriya, Tunji Disu. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Twitter

An kwato bindigar Ak-47

Bayan an hallaka mutanen biyu, jami'an sun gudanar da bincike a jikinsu, inda suka sami bindiga kirar AK-47 guda daya tare da akwatin harsashi, wayoyin salula guda biyu, jakunkuna da ake zargin kudin fansa ne a ciki.

Punch ta rahoto Babaseyi ya kara da cewa an kai gawarwakin masu laifin asibitin gwamnati don gudanar da gwaji, alhali ana kara kokarin cafke sauran 'yan bindigar da suka tsere.

An kama mutum 560 a Abuja

A wani labarin, mun kawo muku cewa rundunar 'yan sandan FCT, Abuja ta kama mutum sama da 500 da ake zargi da aikata laifuffuka.

Hakan na zuwa ne bayan dakarun rundunar daka yankuna da dama sun yi wani gangami na musamman domin kakkabe masu laifi daga FCT.

Bayan cafke mutum 560, rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa wannan somin tabi ne, domin za ta cigaba da farautar bata gari a sassan birnin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng