Yadda Barazanar Iran Ta Sanya Trump Yin Basaja bayan Kammala Taron NATO
- An ce Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi amfani da tsohon jirgin shugaban kasa saboda dalilan tsaro sakamakon rikicin Iran
- Sabon jirgin da Qatar ta bai wa Amurka an tura shi zuwa Ingila kafin shugaban kasar ya isa can a tsohon jirgi na Air Force One
- Trump ya ce babu wata sabuwar barazana kai tsaye, amma ya amince cewa halin da ake ciki da Iran na iya janyo damuwar tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washigton, Amurka - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bar taron kungiyar NATO da aka gudanar a Turkiyya cikin tsohon jirgin shugaban kasa.
Shugaba Trump ya tafi a tsohon jirgi ne yayin da aka tura sabon jirgin da Qatar ta bai wa Amurka zuwa Ingila tun kafin isowarsa.

Source: Getty Images
Rahoton CNN ya ce wasu jami'an gwamnatin Amurka hudu sun nuna cewa an dauki wannan mataki ne a wani bangare saboda damuwar tsaro da ta taso sakamakon rikicin da ke kara kamari tsakanin Amurka da Iran.
Wasu daga cikin jami'an sun bayyana cewa jami'an tsaro sun fi amincewa shugaban ya yi tafiya a tsohon jirgin, wanda aka kera tun daga farko da nufin kare lafiyar shugaban kasa.
Sabon jirgin saman wanda kudinsa sun kai $400m kuwa an gyara shi ne bayan da kasar Qatar ta bayar da shi kyauta ga Amurka.
Damuwar tsaro bayan rikicin Iran
Majiyoyin sun ce babu wata sabuwar barazana kai tsaye ga rayuwar Trump.
Sai dai shugaban ya ambaci yiwuwar Iran ta yi yunkurin kashe shi yayin taron NATO, bayan hare-haren da Amurka ta kai kan Iran, kasar da ke makwabtaka da Turkiyya.
"Ni ne mutum na farko a jerin wadanda ake son kashewa," in ji Trump.
Jaridar The New York Times ta riga ta wallafa rahoto kan damuwar tsaron, yayin da CNN ta nemi Fadar White House ta yi karin bayani.
Wata majiya ta ce:
"Kimanta barazanar tsaro tana sauyawa lokaci zuwa lokaci."
An tura sabon jirgin zuwa Ingila tun da wuri
Kafin Trump ya bar taron NATO a Turkiyya, jami'ai sun tura sabon jirgin da Qatar ta bayar zuwa sansanin sojin saman Amurka da ke Mildenhall a Ingila.
Trump ya rubuta a shafinsa na sada zumunta cewa an yi hakan ne domin sojojin Amurka da ke sansanin su samu damar zagayawa cikin jirgin.
"Kowa na cikin farin ciki, kuma mun ga ya dace su kasance na farko da za su ga jirgin."
- Shugaba Donald Trump
Trump ya ba da bayanai mabambanta
Da ya isa Ingila, Trump ya sauya jirgi a wani sansanin sojin Amurka da ke da matakan tsaro. Da aka tambaye shi dalilin sauya jirgin, ya ce:
"Ba wata damuwar tsaro ba ce. Mun dai tura jirgin ne da wuri domin su samu damar ganinsa."
Sai dai daga baya, lokacin da aka tambaye shi dalilin da ya sa aka umarci 'yan jaridar da ke cikin jirgin su rufe labulen tagogi yayin tashinsa daga Ankara, Trump ya ce yiwuwar barazanar da ke da alaka da Iran na iya zama daya daga cikin dalilan.

Source: Getty Images
Ya ce jirgin Air Force One na iya kasancewa cikin hadari saboda mutanen da ya bayyana a matsayin masu mugun nufi.
"Mutane ne masu hatsarin gaske, don haka zan iya fahimtar irin wannan damuwa."
- Shugaba Donald Trump
Trump ya kara da cewa bai san cewa an bai wa 'yan jaridar wannan umarni na rufe labulen tagogi ba.
Trump ya yi barazana ga Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasae Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar daukar matakin soja mai tsanani idan Iran ta sake kai hari.
Shugaba Donald Trump ya yi barazanar cewa duk wani hari da Iran za ta kai, Amurka za ta yi ramuwar gayya har sau 20.
Asali: Legit.ng


