Babbar Magana: Sojojin Isra'ila Sun Tsare Sheikh Mohammed Hussein bayan Sallar Juma'a
- Sojojin Isra'ila sun tsare babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Mohammed Hussein, bayan ya jagoranci sallar Juma’a a Masallacin Al-Aqsa
- Rahotanni sun nuna cewa bayan sojojin sun sake shi, gwamnatin Isra'ila ta hana shi shiga harabar Masallacin Al-Aqsa na tsawon mako guda
- Mahukuntan Falasdinu sun ce matakin na zuwa ne yayin da hare-hare da kutsen Isra’ila ke karuwa a wurin mai tsarki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Isra'ila - Rahotanni sun nuna cewa dakarun sojojin Isra'ila sun cafke Babban Muftin Kudus, Sheikh Mohammed Hussein jim kadan bayan ya kammala sallar Jumu'a a masallacin Al-Aqsa.
Bayanai sun nuna cewa sojojin na kasar Yahudawa sun saki babban malamin musuluncin bayan sun tsare shi da ɗan lokaci.

Source: Getty Images
Isra'ila ta hana malamin shiga Al-Aqsa
Tashar Al-Jazeera ta rahoto cewa mahukuntan Isra’ila sun sanar da hana Babban Muftin Kudus, Sheikh Mohammed Hussein, shiga harabar Masallacin Al-Aqsa na tsawon mako guda.
Isra'ila ta dauki wannan matakin ne bayan tsare shi da aka yi, kamar yadda Hukumar Gwamnatin Kudus ta bayyana.
A cikin wata sanarwa, ta ce jami’an tsaron Isra’ila sun kama Sheikh Hussein ne bayan ya gabatar da hudubar Juma’a tare da jagorantar sallar Juma’a a Masallacin Al-Aqsa da ke Gabashin Kudus da Isra’ila ta mamaye.
Ta ce daga bisani mahukuntan Isra’ila sun sake shi, amma suka ba shi umarnin kada ya shiga harabar Masallacin Al-Aqsa na tsawon mako guda.
Me yasa Isra'ila ta dauki matakin?
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, rundunar ‘yan sandan Isra’ila ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.
Sai dai a shekarun baya, mahukuntan Isra’ila sun sha kakaba irin wannan takunkumi ga limamai da masu wa’azi a Masallacin Al-Aqsa.
Tun da farko a ranar Juma’a, dubban Falasdinawa sun gudanar da sallar Juma’a a harabar Masallacin Al-Aqsa, cewar rahoton Middle East Eye.

Source: Getty Images
Kutsen Isra’ila a Al-Aqsa ya karu
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da zargin Isra’ila da kara kutsawa cikin harabar Masallacin Al-Aqsa.
A wani rahoto da Ma’aikatar Harkokin Addini da Waqafi ta Falasdinu ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana cewa jami’an Isra’ila sun gudanar da kutse sau 26 cikin harabar Masallacin Al-Aqsa a watan Yuni.
Rahoton ya ce yahudawa 4,212 sun shiga harabar masallacin ta kofar Mughrabi a lokutan ziyara na safe da rana, karkashin kariyar jami’an tsaron Isra’ila.
Isra'ila t shirye bijirewa umarnin Amurka
A wani rahoton, kun ji cewa ministan tsaron Israila, Israel Katz, ya yi maganar janye dakarun sojojin kasarsa daga Kudancin Lebanon da ake yaki da Hezbollah.
Israel Katz ya bayyana cewa dakarun sojojin Israila ba za su bar yankin Kudancin Lebanon ba ko da kuwa kasar Amurka ta bukaci hakan.
Wannan na zuwa ne yayin da aka fara musayar yawu kan zargin karya yarjejeniyar Amurka da Iran, wacce ake ganin ta kunshi tsagaita wuta a Lebanon.
Asali: Legit.ng

