Magana Ta Fito: An Gano Waɗanda Matashi Ya Yi Niyyar Kashewa a Harin Amurka

Magana Ta Fito: An Gano Waɗanda Matashi Ya Yi Niyyar Kashewa a Harin Amurka

  • Matashin da ya kai hari wajen liyafa a Washington ya yi magana bayan cafke shi da jami'an tsaro suka yi a yau Lahadi
  • Maharin ya bayyana waɗanda ya yi yunƙurin kashewa yayin harin da ya tayar da hankula da martani daga kasashen duniya
  • Rahotanni sun nuna cewa ya zo da makamai da dama, ya yi kokarin shiga cikin dakin taro amma jami’an tsaro sun dakile shi kafin ya aikata mummunar barna

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Wani mutum mai suna Cole Tomas Allen, mai shekaru 31, ya kai hari wajen wani taro a Washington, inda ya nufi jami’an gwamnatin Donald Trump.

Rahotanni sun ce Allen ya shaida wa ‘yan sanda cewa yana son kai farmaki kan jami’an gwamnati da ke cikin liyafar da aka shirya a otel din Washington Hilton.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Martanin Netanyahu kan harin da aka yi yunkurin kashe Trump, matarsa

An tatsi bayanai daga matashin da ya kai hari a White House
Cole Tomas Allen da ake zargin ya kai wa su Trump hari, Donald Trump Hoto: Find Richard Holliday /Donald J Trump.
Source: Getty Images

Sai dai jami’an tsaro sun bayyana cewa ba a tabbatar da cewa yana son kashe Trump kai tsaye ba, amma yana kokarin kai hari ga duk wanda ya samu, cewar New York Post.

Yadda matashi ya kutsa fadar White House

Wani jami’in tsaro ya ce Allen na kokarin kutsawa cikin taron ne domin ya kai hari ba tare da la’akari da wanda zai samu ba.

Mataimakin daraktan Secret Service ya ce harin na iya zama babban bala’i na kasa, amma tsaron da aka tanada ya dakile shirin tun farko.

Rahotanni sun bayyana cewa Allen ya zo da bindiga, wuka da sauran makamai, inda ya yi kokarin shiga cikin dakin taro mai dauke da mutane kusan 2,500.

An ce ya samu shiga otel din ne bayan ya biya kudin daki, sannan ya boye makamai kafin daga bisani ya fito da su domin kai hari.

Harin ya faru ne bayan mintuna 20 da shiga Shugaba Trump da matarsa Melania, inda jami’an tsaro suka fitar da su cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Cole Allen: Abubuwan mamaki game da matashin da ya kai hari kan su Donald Trump

Mahari ya fadi wadanda ya yi niyyar kashewa
An kama Cole Tomas Allen, wanda ake zargi da bude wuta a wajen taron cin abincin dare na kungiyar 'yan jaridun fadar White House (WHCA). Hoto: Trump via Truth Social/Anadolu via Getty Images.
Source: Getty Images

Harin ya jikkata wani jami'in DSS

Wani jami’in DSS ya jikkata yayin musayar wuta, amma an kai shi asibiti kuma yana cikin yanayi mai kyau kamar yadda Trump ya bayyana.

An tuhumi Cole Allen da amfani da makami wajen aikata laifi da kuma kai hari ga jami’in gwamnati, yayin da bincike ke ci gaba da gano dalilin harin.

Jami’ai sun ce Allen ya yi tafiya daga Los Angeles zuwa Washington ta jirgin kasa, kuma ana duba ko hakan yana da alaka da kokarinsa na boye motsinsa.

Trump ya bayyana cewa bai yi imanin harin yana da alaka da rikicin Amurka da Isra’ila da Iran ba, yana mai cewa hakan ba zai hana shi ci gaba ba.

Netanyahu ya yi fusata da hari kan Trump

An ji cewa shugabannin duniya sun nuna goyon baya ga Donald Trump bayan harin bindiga a liyafar manema labarai ta Fadar White House

Kara karanta wannan

Bayan ta da hankalin Trump da matarsa, an gano wanda ya kai hari yayin liyafa

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da wasu shugabanni sun bayyana firgici kan harin, suna yaba wa jami’an tsaro kan gaggawar dakile maharin.

Shugabannin kasashe kamar Indiya, Pakistan da Taiwan sun yi Allah wadai da tashin hankali a siyasa, suna addu’ar samun lafiya ga jami’in dan sanda da ya jikkata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.