Yadda 'Yan Bangar Siyasa Suka Hallaka Wani Fitaccen Malamin Islamiyya a Bauchi

Yadda 'Yan Bangar Siyasa Suka Hallaka Wani Fitaccen Malamin Islamiyya a Bauchi

  • Wasu da ake zargin ƴan daba ne sun kashe fitaccen malamin Islamiyya, Malam Rilwanu Dauda, a Bauchi bayan saɓani kan fastocin siyasa
  • Iyalan mamacin sun buƙaci gwamnati da 'yan sanda su kamo waɗanda ake zargi domin a hukunta su don ganin an bi kadin d'an uwansu
  • Wasu mazauna unguwar Karofin Madaki sun bayyana marigayin a matsayin mutum mai kirki, mai tausayi da son zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Bauchi - Mazauna unguwar Karofin Madaki da ke cikin birnin Bauchi sun shiga jimami bayan kashe fitaccen malamin Islamiyya, Malam Rilwanu Dauda.

Rahotanni sun bayyana cewa ana zargin wasu ƴan daba masu alaƙa da siyasa ne suka hallaka fitaccen malamin.

'Yan dabar siyasa sun hallaka wani malamin Islamiyya a Bauchi
Taswirar jihar Bauchi inda aka kashe wani malamin Islamiyya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

An kashe malamin Islamiya a Bauchi

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa an kashe Malam Rilwanu mai shekaru 42 a ranar Lahadi, bayan wata hatsaniya da ta samo asali kan liƙa fastocin siyasa a kusa da gidansu.

Kara karanta wannan

Ana sayar da Kiristocin Arewa a matsayin bayi a Najeriya? An ji gaskiyar zance

An ce marigayin ya samu rauni mai tsanani bayan da aka caka masa wuƙa a ciki, lamarin da ya yi sanadin rasuwarsa kafin ya isa Asibitin Kwararru na Jihar Bauchi.

Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya fara ne da misalin ƙarfe 10:00 na safe, lokacin da marigayin ya nemi wasu matasa da ake zargi ƴan daba ne su cire fastocin siyasa da suka liƙa a wani allo da ke kusa da gidan iyalansu.

Sai dai matasan sun ƙi cire fastocin, lamarin da ya rikide zuwa faɗa.

Yadda 'yan daba suka kashe malamin

Ɗan'uwan mamacin, Hamza Dauda, ya ce ƙarami daga cikin waɗanda ake zargin ya baga wa marigayin sanda, yayin da babban ya buga masa wuƙa a kai, abin da ya sa ya faɗi ƙasa.

Ya ce bayan mutane sun shiga tsakani aka tarwatsa su, ɗaya daga cikin matasan ya koma gidansu, ya ɗauko wuƙa sannan ya dawo ya caka wa Malam Rilwanu ita a ciki kafin ya gudu.

Hamza ya ce mutanen da ke wurin ne suka garzaya da shi asibiti, amma an tabbatar da rasuwarsa kafin ya iya samun dauki daga likitoci.

Kara karanta wannan

Kaduna ta ɗauki zafi, mutanen gari sun sake kama mutum 2 sun masu kisan gilla

Iyalai sun nemi a yi musu adalci

Jaridar Daily Trust ta rahoto ta rahoto Hamza ya bayyana cewa marigayin mutum ne mai son zaman lafiya wanda ba ya faɗa da kowa.

Iyalan malamin islamiyya da aka kashe sun roki gwamnatin Bauchi da 'yan sanda su tabbata an kamo masu laifin
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed yana jawabi a fadar gwamnati. Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Facebook

Ya roƙi gwamnati da rundunar 'yan sanda su gaggauta kamo waɗanda ake zargi tare da gurfanar da su a kotu.

A cewarsa, iyalan mamacin na son a tabbatar an yi adalci saboda an kashe ɗan uwansu ba tare da wani laifi ba.

Har zuwa lokacin da aka ziyarci gidan mamacin, jama'a na ci gaba da tururuwar zuwa yin ta'aziyya, kwanaki huɗu bayan aukuwar lamarin.

Wasu mazauna yankin sun bayyana marigayin a matsayin mutum mai mutunci, tausayi da karamci.

Mutane sun kashe malamar Islamiyya

A wani labari, mun ruwaito cewa, wasu mutane sun kashe wata mata da aka ce malamar Islamiyya ce tare da kona gawarta a Maraban Jos a jihar Kaduna.

An bayyana cewa da farko ta shiga ofishin 'yan sanda amma tarin mutane suka mamaye shi, suka fitar da ita, suka kashe ta kan zargi maras tushe.

Biyo bayan lamarin, rundunar 'yan sandan Kaduna ta ce ta kama wasu mutane inda ta ce za a hukunta wanda aka samu da laifi ba sani ba sabo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com