Wike Ya Tsage Gaskiya kan Yiwuwar PDP Ta Iya Lashe Zaben Shugaban Kasa a 227
- Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya ce PDP ba za ta iya lashe zaben shugaban kasa ba sai ta gyara rikicin cikin gida
- Wike ya bayyana cewa wajibi ne jam'iyyar ta gyara tsarinta na cikin gida tun daga matakin mazabu har zuwa kasa kafin zaben 2027
- Ministan ya ce abin da ya fi muhimmanci shi ne gina jam'iyya daga matakin kasa, tare da samun nasarori a jihohi kafin a fara tunanin karbe mulkin kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa zai yi wahala jam'iyyar PDP ta sake lashe zaben shugaban kasa a 2027 a halin da take ciki.
Wike ya bayyana cewa babu ta yadda PDP za ta iya lashe zabe matukar ba ta fara gyara tsarinta na cikin gida da warware rikice-rikicen da ke addabarta ba.

Source: Facebook
Wike ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai ranar Alhamis, 9 ga watan Yulin 2026, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.
Tsohon gwamnana na jihar Ribas ya ce babu wata jam'iyyar siyasa da za ta iya cin zaben shugaban kasa idan ba ta fara gina kanta daga tushe ba.
PDP na bukatar sake gina kanta
Wike ya amince cewa PDP na fuskantar matsaloli masu yawa, yana mai cewa sake mayar da jam'iyyar kan hanyar samun nasara a zaben shugaban kasa ba abu ne mai sauki ba.
Ya ce:
"Na fada cewa PDP tana da matsala. Idan kana da irin wannan matsalar, ba abu ne mai sauki ka dawo ka lashe zaben shugaban kasa ba.
"Ba ma batun zaben shugaban kasa kadai. Har gudanar da zaben mazabu ma yana da wahala."
Mafitar da Wike ya hango ga PDP
Ministan ya ce abin da ya fi muhimmanci shi ne gina jam'iyya daga matakin kasa, tare da samun nasarori a jihohi kafin a fara tunanin karbe mulkin kasa.

Kara karanta wannan
Gwamnatin tarayya ta yi wa sojoji ƙarin lbashi mai gwaɓi don inganta walwalarsu a Najeriya
Ya ce:
"Abin da ya fi muhimmanci shi ne ku gina jam'iyya, ku nuna abin da za ku iya yi a matakin jiha, ku tattara kuri'un da za ku iya samu, sannan ku hada karfi ku shirya."
Wike ya ce samun nasara a zaben shugaban kasa na bukatar tsari mai karfi da kuma shiri na dogon lokaci, cewar rahoton Vanguard .

Source: Twitter
Shin Wike na yiwa APC aiki?
Ministan na Abuja ya kuma yi martani kan zarge-zargen da aka taba yi masa cewa yana yi wa jam'iyyar APC aiki.
Ya ce:
"Ba ni ne aka rika cewa wakilin APC ba? Ina masu wannan zargin yanzu? Har yanzu ina nan, ban taba boye matsayina ba. Na dade ina fadawa jam'iyyarmu cewa mu gyara gidanmu."
Saƙon Wike ga 'yan takarar PDP
A wani labarin, kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike , ya buƙaci mambobin jam'iyyar PDP da su shiryawa gagarumin yaƙin siyasa gabanin babban zaɓen 2027.
Wike ya bayyana cewa ba a taɓa bayar da mulki haka kawai, sai dai ana samunsa ne ta hanyar fafutuka, sadaukarwa, da kuma aiki tuƙuru.
Ya shaida wa magoya bayan PDP cewa siyasar adawa tana buƙatar juriya, tsari, da kuma ƙuduri, inda ya yi gargaɗin cewa jam'iyyarNba za ta koma kan mulki ta hanyar takama ko tunani kawai ba.
Asali: Legit.ng

