Yana Ajiye Mukamin Minista, Tuggar Ya Fadi abin da Ya Jawo Ta'addanci a Bauchi

Yana Ajiye Mukamin Minista, Tuggar Ya Fadi abin da Ya Jawo Ta'addanci a Bauchi

  • Tsohon Ministan Harkokin Waje, Yusuf Maitama Tuggar, ya bayyana wasu matsaloli biyu da ya ce su ne suka jawo karuwar ta'addanci a Bauchi
  • Yayin da Tuggar ya tabo batun rikicin manoma da makiyaya, tsohon ministan ya jadda cewa kiwo sana'a ce da ake yi har a kasashen da suka ci gaba
  • Ya kuma bayyana cewa rashin biyan tsofaffin ma'aikata haƙƙoƙinsu na fansho da garatuti a matsayin dalilin jefa iyali zuwa ga ayyukan ta'addanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Bauchi – Yusuf Maitama Tuggar, wanda ke neman takarar gwamnan jihar Bauchi a zaɓen 2027, ya fito fili ya bayyana ra’ayoyinsa kan matsalolin da suka dabaibaye jihar, musamman ta fuskar rashin tsaro.

A wata tattaunawa ta musamman da ya yi da manema labarai a ranar Lahadi, Tuggar ya ba da haske kan yadda rashin adalci wajen raba filaye da kuma nuna kyama ga tsarin kiwo na gargajiya suke zama barazana ga zaman lafiya a jihar.

Kara karanta wannan

Yusuf Tuggar, ministan Tinubu da ya yi murabus ya ayyana shiga takarar gwamna

Tsohon minista, Yusuf Tuggar ya bayyana dalilan da ke jawo ta'addanci a Bauchi.
Yusuf Tuggar, tsohon ministan harkokin wajen Najeriya da ya shiga takarar gwamnan Bauchi. Hoto: @YusufTuggar
Source: Twitter

Abin da ke jawo ta'addanci a Bauchi

Tsohon ministan ya bayyana cewa ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ke rura wutar garkuwa da mutane da fashi da makami shi ne takun-saka tsakanin manoma da makiyaya wanda ya samo asali daga rabon filaye, in ji rahoton Punch.

Ya bayyana cewa yadda ake danne haƙƙin makiyaya ta hanyar toshe burtalai da raba gonaki ba tare da lura da wuraren kiwo ba, ya sanya mutane da dama jin cewa an yi watsi da su.

"Kiwo tsari ne na rayuwa kuma bai saɓa da tsarin zamani ba. Akwai makiyaya a ƙasashen da suka ci gaba, don haka ba alamar rashin wayewa ba ne."

- Yusuf Tuggar.

Ya ƙara da cewa karuwar yawan jama'a da kuma yadda ake raba filaye ga manyan mutane waɗanda ba sa ma yin noma a kai, yana korar ƙananan manoma da makiyaya daga hanyoyin neman abincinsu, wanda hakan ke tura su shiga ayyukan laifi.

Kara karanta wannan

Gwamna zulum ya fadi manyan dabaru 2 da ke ba ƴan ta'adda damar kai wa sojoji hari

Hanyar dakile ta'addanci a Bauchi

Baya ga batun filaye, tsohon ministan ya bayyana cewa rashin biyan ma'aikata haƙƙoƙinsu bayan sun yi ritaya ba wai kawai zalunci ba ne ga ma'aikacin, a'a, barazana ce ga tsaron ƙasa baki ɗaya.

"Biyan fansho da garatuti babban al'amari ne ga rayuwar mutane da kuma tabbatar da kwanciyar hankali a cikin al'umma. Idan aka yi watsi da iyalai, rashin tsaro zai ci gaba da girma a faɗin jihar."

- Yusuf Tuggar.

Tuggar ya yi alƙawarin cewa idan ya zama gwamna, biyan waɗannan haƙƙoƙin zai zama ɗaya daga cikin manyan ginshiƙan da gwamnatinsa za ta mayar da hankali a kai.

Yusuf Tuggar ya nuna hanyoyin kawo karshen matsalar tsaro a Bauchi
Taswirar jihar Bauchi, inda 'yan bindiga suka fara addabar mutanen karkara. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Shirin bunkasa tattalin Bauchi

A ƙarshe, Yusuf Tuggar ya zayyana cewa ba za a iya samun tsaro mai ɗorewa ba har sai an samar da ayyukan yi waɗanda suka dace da zamani in ji rahoton This Day.

Ya bayyana fannin noma, hakar ma'adinai, da kuma amfani da fasahar zamani wajen samar da ayyukan yi a matsayin hanyoyin da yake shirin bi domin rage raɗadin talauci a jihar Bauchi.

Kara karanta wannan

Tinubu ya nada sababbin ministoci 2 da ya fatattaki Wale Edun da Ahmed Dangiwa

Ya ce burinsa shi ne samar da gwamnati mai tafiya da kowa ba tare da nuna wariya ba ga kowane ɓangare na al'umma.

Tuggar ya ayyana shiga takarar gwamna

A wani labari, mun ruwaito cewa, tsohon minista, Yusuf Maitama Tuggar, ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Bauchi a zaɓen 2027.

Yusuf Tuggar, wanda tsohon ɗan majalisar wakilai ne, ya bayyana cewa bai fito neman takarar gwamna domin ya gina kansa ba, sai don gina al'umma.

Tsohon ministan ya lashi takobin ba wasu fannoni hudu muhimmanci da za su iya canja tarihin jihar Bauchi idan ya sami nasara a zaben na 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com