Kisan Khamenei: Amurka da Israila na cikin Matsala, Babban Kwamandan IRGC Ya Sha Alwashi

Kisan Khamenei: Amurka da Israila na cikin Matsala, Babban Kwamandan IRGC Ya Sha Alwashi

  • Babban kwamandan IRGC, Birgediya Janar Ahmad Vahidi ya ce za a dauki fansa kan Amurka da Isra'ila saboda kashe Ayatollah Ali Khamenei
  • Birgediya Janar Ahmad Vahidi ya jaddada cewa neman adalci da hukunta masu hannu a kisan zai ci gaba har sai an cimma buri
  • Vahidi ya bayyana cewa wannan lamari ba zai taba gogewa daga tarihin al'ummar Musulmi da bangaren gwagwarmaya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tehran, Iran - Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC), Birgediya Janar Ahmad Vahidi, ya sha alwashin daukar fansa kan Amurka da Isra'ila.

Birgediya Janar Ahmad Vahidi ya sha alwashin daukar fansar ne bayan kashe Jagoran addini a Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

Ahmad Vahidi ya sha alwashin daukar fansa kan kisan Ali Khamenei
Birgediya Janar Ahmad Vahidi da Shugaba Donald Trump na Amurka Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A wata sanarwa da tashar Press tv ta wallafa, Vahidi ya ce kisan Khamenei ba zai taba gogewa daga tarihin al'ummar Musulmi da bangaren gwagwarmaya ba.

Kara karanta wannan

Sakon gwamnan Kano, Abba Gida Gida ga lauyoyi game da zaben 2027

Vahidi ya nemi hukunta wadanda ke da hannu

Vahidi ya yi kira da a tabbatar da adalci tare da daukar matakin da ya dace kan wadanda ya zarga da aikata laifin.

"Dole ne a tabbatar da cikakken adalci tare da daukar matakin da ya dace kan masu laifi, musamman sojojin Amurka masu kashe yara."

- Birgediya Janar Ahmad Vahidi

Ya kara da cewa shugabannin Amurka da sauran makiyan Juyin Juya Halin Musulunci kada su yi zaton cewa kashe jagoran zai karya ruhin gwagwarmaya.

"Shugabannin masu laifi na Amurka da duk makiyan Juyin Juya Halin Musulunci da bangaren gwagwarmaya su sani cewa ta hanyar wannan kisan na rashin jarumtaka ba za su iya kashe hasken Allah ba, ko raunana kudurin al'ummomi masu imani, ko kuma sauke tutar gwagwarmaya."

- Birgediya Janar Ahmad Vahidi

"Neman adalci ba zai kare ba"

Vahidi ya ce jinin Khamenei ya dora nauyi a kan dukkan masu son 'yanci a duniya na neman adalci da hukunta wadanda suka aikata, suka bayar da umarni ko suka mara wa wannan hari baya.

Kara karanta wannan

Sarkin Zazzau ya ba da shawara kan gudanar da sahihin zabe a Najeriya

Babban kwamandan na IRGC ya jaddada cewa wannan bukata za ta ci gaba da kasancewa halal kuma ba za a manta da ita ba, rahoton Aljazeera ya tabbatar da hakan.

A cewarsa:

"Neman daukar fansa ga shahidai da hukunta masu hannu a wannan laifi zai ci gaba da kasancewa tabbatacciyar bukata ta halal wadda ba za a taba mantawa da ita ba."
Ahmad Vahidi ya sha alwashin daukar fansa
Ahmad Vahidi a wajen janaizar Ayatollah Ali Khamenei Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An binne Khamenei a Mashhad

Kalaman Ahmad Vahidi sun zo ne bayan an binne Ayatollah Ali Khamenei a garinsu na Mashhad ranar Alhamis, 9 ga watan Yulin 2026.

An binne shi ne watanni hudu bayan da shi da mutum hudu daga cikin iyalansa suka mutu sakamakon hare-haren sama da Amurka da Isra'ila suka kai.

Amurka ta kashe sojojin Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa ​​​​​​​​​​​​​​gwamnatin Iran ta tabbatar da cewa sojojin kasar takwas sun rasa rayukansu sakamakon wasu sababbin hare-haren da Amurka ta kai Kudancin kasar.

Sojojin da aka kashe sun kasance jami'an rundunar sojin sama da ta ruwa ta Iran bayan an kai hare-hare kan biranen Bandar Abbas da Bushehr.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng