'Yan Bindiga Sun Shiga Kano da Makamai cikin Dare, Sun Yi Kisa
- Rahoto ya nuna cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai mummunan hari jihar Kano, inda suka kashe rai da jikkata mutane
- Shugaban 'yan sa-kai na yankin da abin ya faru ya tabbatar da faruwar harin, inda ya yi kira ga hukumomi kan daukar matakin gaggawa
- Hare-haren 'yan bindiga na cigaba da karuwa a kwanan nan a fadin Najeriya, duk da cewa sojoji na kai musu farmaki ba kakkautawa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai wani mummunan hari a Karamar Hukumar Rogo a Jihar Kano, inda suka kashe mutum guda tare da jikkata wasu da dama, lamarin da ya sa aka kara tsaurara matakan tsaro a yankin.
Harin ya faru ne a daren ranar Alhamis a kauyen Barbaji da ke gundumar Jajaye, inda rahotanni suka nuna cewa wasu mutane hudu dauke da makamai sun kutsa cikin jama'a da misalin karfe 9:00 na dare.

Kara karanta wannan
Rashin imani: Bam ya tashi da mutane da yawa, yan ta'adda sun bi su da harbi a Borno

Source: Original
Yadda 'yan bindiga suka kai hari Kano
Tribune ta rahoto cewa maharan sun iso ne kan babura, sanye da kayan jami'an tsaro, kuma sun nufi wani dan kungiyar tsaro ta sa-kai mai suna Alasan Yellow.
Shaidu sun bayyana cewa an harbe mutumin ne a kusa da shi a gaban shagonsa, lamarin da ya jefa al’umma cikin firgici. A cikin rikicin da ya biyo baya, an harbi wani mutum da ya yi kokarin shiga tsakani.
Bayan haka, maharan sun wuce zuwa ofishin kungiyar ‘yan sa-kai na yankin inda suka rika harbe-harbe ba tare da kakkautawa ba, wanda ya tilasta wa mazauna yankin tserewa domin tsira da rayukansu.
Bayanin 'ya sa kai kan harin Kano
Kwamandan kungiyar ‘yan sa-kai ta Rogo, Alhaji Haruna Barhaya, ya tabbatar da aukuwar harin yayin da yake yi wa hukumomin yankin bayani.
Rahotanni sun nuna cewa Alhaji Haruna Barhaya ya ce mutum guda ya mutu nan take, yayin da wasu da dama suka samu raunuka.
“Mutane hudu daga cikin wadanda aka jikkata na karbar magani a halin yanzu bisa raunuka daban-daban,”
In ji shi, yana mai cewa daukar matakin gaggawa da jami’an tsaro na yankin suka yi ya taimaka wajen hana karin asarar rayuka.
Matakin da aka dauka bayan harin
Daily Post ta wallafa cewa mambobin kungiyar ‘yan sa-kai tare da hadin gwiwar jami’an tsaro sun kwashe wadanda suka jikkata zuwa asibitocin da ke kusa.
An mayar da daya daga cikin wadanda suka ji rauni mai tsanani wani asibiti a yankin Gwarzo domin samun kulawa ta musamman.

Source: Facebook
Tuni hukumomi suka kara tsaurara tsaro a yankin, inda aka tura rundunar sintiri ta hadin gwiwa daga Karamar Hukumar Kiru da wasu sassan Jihar Kaduna.
'Yan bindiga sun kashe basarake
A wani labarin, mun kawo muku cewa wasu 'yan bindiga dauke da makami sun kai mummunan hari jihar Benue, inda suka jawo asarar rai.
An bayyana cewa maharan da suka yi yaren mutanen yankin kafin bude wuta sun kashe wani basarake, matar shi da kuma dan shi.
Wasu rahotanni da aka samu daga yankin da abin ya faru sun nuna cewa maharan sun wuce wani gida inda suka kashe wani mutun daya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
