An Gwabza Fada tsakanin Sojoji da Boko Haram, an Kona Wurare a Borno
- Rahoto ya ce mayakan ISWAP sun kai hari a sansanin soji da ke Logomani a karamar hukumar Ngala jihar Borno da daddare
- An kashe soja daya a harin, sannan mayakan sun kone ofishin 'yan sanda, asibitin kiwon lafiya da ajujuwa a makaranta
- Dakarun Operation Hadin Kai sun farmaki 'yan ta'addan bayan harin, kuma an aika da ƙarin sojoji domin ƙarfafa tsaron wurin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Borno - Mayakan ISWAP sun kai hari a sansanin soji da ke ƙauyen Logomani a karamar hukumar Ngala ta jihar Borno a daren ranar Talata.
Bayan sun kai farmaki a sansanin soji, 'yan ta'addan sun watsa mazaunan ƙauyen ta hanyar harbin bindiga kafin su kona wasu muhimman gine-gine a yankin.

Source: Original
Rahoton Punch ya nuna cewa abubuwan da aka ƙone sun haɗa da ofishin 'yan sanda, cibiyar kiwon lafiya da kuma ajujuwa biyu a wata makarantar firamare.
An raunata sojoji a Borno
Kyaftin Muhammed Goni, wanda ke aiki a matsayin jami'in watsa labarai na hedikwatar rundunar Operation Hadin Kai a Arewa maso Gabas, ya tabbatar da aukuwar wannan farmaki a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.
A cewarsa, ko da yake 'yan ta'addan sun sami damar shiga wani gefen ganuwar tsaron sansanin a tsakiyar faɗan, sai dai dakarun suka sake tattara kansu cikin gaggawa suka kori maharan da ƙarfi.
Rahotannin da sojoji suka fitar sun nuna cewa an yi wa 'yan ta'addan raunuka masu yawa, kuma suka gudu da suka ji wuta.
Daga cikin sanarwar akwai cewa:
"Soja daya da ya nuna jarumta ya rasu, yayin da aka yi wa manyan motoci biyu da wasu kayan aiki lahani a lokacin faɗan."
Kyaftin Goni ya ƙara da cewa an ƙarfafa tsaron sansanin ta hanyar aika da ƙarin dakarn, kuma cigaba da bibiyar 'yan ta'addan a yanzu haka.

Source: Facebook
Matakin da hukuma ta dauka
A ranar Laraba, shugaban karamar hukumar Ngala, Mala Tijjani Ngala, ya ziyarci Logomani domin ganin yadda abubuwa suke gudana.
Hn. Mala Tijjani Ngala ya duba ofishin 'yan sanda da aka lalata, asibitin da aka ƙone da kuma makarantar firamare.
Shugaban karamar hukumar ya ce za a tura rahoto zuwa ga gwamnatin jihar Borno domin a dauki matakin gyarawa. Haka zalika ya yi kira ga mazaunan da su yi haƙuri su kuma ba wa hukumomin tsaro haɗin kai.
Daily Post ta wallafa cewa kakakin 'yan sanda na Borno ASP Nahum Daso bai yi martani ba lokacin da aka yi ƙoƙarin tuntuɓarsa.
An yi taro kan tsaro a Kaduna
A wani labarin, mun kawo muku cewa gidauniyar mai alfarma Sarkin Musulmi ta hada zama na musamman da masu ruwa da tsakin Arewa kan matsalar tsaro.
Taron ya hada manyan malaman Arewacin kasar nan, ciki har da Sheikh Abdullahi Bala Lau da sauran wakilan kungiyoyin addini daban-daban.
Manyan sarakuna da suka hada da Shehun Borno da Sarkin Zazzau sun halarci zaman da aka yi domin lalumo hanyar yaki da matsalolin Arewa.
Asali: Legit.ng

