Trump: "Dalilin da Ya sa ake Yawan Kawo Mani Hari"

Trump: "Dalilin da Ya sa ake Yawan Kawo Mani Hari"

  • Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi magana game da yawan hare-hare da matasa dauke da bindigu ke yunkurin kai masa
  • Ya yi wannan bayani ne bayan an kama wani matashi, Cole Tomas Allen da ake zargi ya yi yunkurin kai wa Trump hari a Washington
  • Shugaban kasar ya bayyana cewa ko a jikinsa, kuma irin waɗannan hare-hare da ke auna rayuwarsa ba za su hana aiki ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

United States– Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana abin da ya sa ake yawan kai masa hare-hare da bindigu a ƙasarsa.

Ya ce yana kallon hare-haren a matsayin wata alama ta irin tasirin da yake da shi a tarihi, yana mai cewa ba zai bari irin wannan barazana ta tsoratar da shi ko ta hana shi aiki ba.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: An gano waɗanda matashi ya yi niyyar kashewa a harin Amurka

Shugaba Donald Trump ya faɗi muhimmancinsa a tarihi
Shugaban Amurka Donald Trump a wani taron kamfen kafin zabensa Hoto: Donald J Trump
Source: Twitter

Washington Post ta wallafa cewa an kai wa Trump hari a wani otal da ke Washington, inda shugaban da wasu manyan jami’an gwamnatinsa suka halarci liyafar ‘yan jarida na Fadar White House.

Harin Trump: Jami'an tsaro sun kama Allen

The Detroit News ta wallafa cewa Shugaban ‘yan sandan birnin Washington na wucin gadi, Jeffery Carroll, ya ce wanda ake zargi ya wuce ta shingen tsaro don shiga dakin da Trump ya ke.

Bayan wannan sabon lamari – wanda ya biyo bayan yunkurin kashe shi sau biyu a lokacin yakin neman zaben 2024 – Trump ya ce ya fara tunanin dalilin da ya sa irin wadannan abubuwa ke yawan faruwa a gare shi.

Trump ya ce:

“Na yi nazari kan kisan shugabanni, kuma zan fada muku, mutanen da suka fi tasiri, wadanda suke yin abubuwa masu girma su ne ake yawan kai wa hari."

Trump ya magantu kan kashe shugabanni

Kara karanta wannan

Cole Allen: Abubuwan mamaki game da matashin da ya kai hari kan su Donald Trump

Ya ambaci tsohon shugaban Amurka Abraham Lincoln a matsayin misali, amma bai ambaci Ronald Reagan ba, wanda aka taba harba a wajen wannan otal din a shekarar 1981.

Trump ya ce yana kokarin kada ya mayar da hankali sosai a kan hadarin da ke tattare da zama shugaban kasa.

A watan Yulin 2024, wani mutum ya harbe shi a kunne yayin gangamin yakin neman zabe a Pennsylvania.

Trump ya ce shugabanni masu tarihi kawai ake kai wa irin wannan hari
Shugaban Masar Amurka Donald Trump Hoto: Donald J Trump
Source: Twitter

A watan Satumba kuma, an gano wani da ya kafa wajen harbin nesa a kusa da filin wasansa na golf a West Palm Beach, Florida, inda jami’an tsaro suka cafke shi.

Amma ya jaddada cewa ba zai bari tsoron tashin hankali ya canza rayuwarsa ko ta wasu ba. Trump ya ce yana son a ci gaba da gudanar da taron, amma jami’an tsaro suka dakatar saboda bukatar a duba wurin.

Abin da aka gano kan harin Trump

A baya, mun wallafa cewa matashin da ya kai hari wajen liyafa a Washington ya yi magana bayan cafke shi da jami'an tsaro suka yi a ranar Lahadi 26 ga watan Afrilu, 2026.

Kara karanta wannan

Bayan ta da hankalin Trump da matarsa, an gano wanda ya kai hari yayin liyafa

Maharin ya bayyana waɗanda ya yi yunƙurin kashewa yayin harin da ya tayar da hankula da martani daga kasashen duniya da ke Allah wadai da yunkurin.

Rahotanni sun nuna cewa ya zo da makamai da dama, ya yi kokarin shiga cikin dakin taro amma jami’an tsaro sun dakile shi kafin ya aikata mummunar barna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng