Bayan Jana'izar Khamenei, an Fara Batun Kashe Trump, Isra'ila Ta Yi Magana
- Kasar Isra'ila ta ba Amurka bayanai na sirri game da zargin shirin Iran na kashe Shugaba Donald Trump a wannan mako
- Wasu jami'an Amurka sun zargi Isra'ila da kai wannan rahoto ne domin tilasta Donald Trump ya ƙarfafa harin soji a Iran
- Amurka da Iran na ci gaba da musayar farmaki bayan tsagaita wuta sakamakon abubuwan da suka faru a mashigar Hormuz
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja - Isra'ila ta ba Amurka wasu bayanan sirri da ke zargin cewa Iran ta tsara sabon shiri na kashe Shugaba Donald Trump.
Daya daga cikin majiyyar ta ce gargadin ya zo a cikin wannan mako, dayar kuma ta ce hukumomin leken asirin Amurka sun riga sun kasance suna bibiyar labaran da ke nuna zaton Iran na shirin kai hari kan jami'ansu.

Source: Getty Images
Martanin wasu jami'an Amurka
CNN ta wallafa cewa wasu jami'an gwamnatin Amurka sun yi shakkar cewa Isra'ila ta fitar da wannan bayanin ne da nufin jan ra'ayin Trump, musamman game da ƙarfafa hare-haren sojoji a Iran.
Har wa yau, rahoton ya nuna cewa jami'an Amurka basu tabbatar da gaskiyar rahoton da kansu ba kafin Isra'ila ta kawo gargadin.
Gargadi kan son kashe Trump
Gwamnatin Amurka ta sha gargadi a baya cewa Iran na iya ƙoƙarin kashe Trump a matsayin ramuwar gayya ga kisan da aka yi wa janar din Iran, Qasem Soleimani a wani farmaki na jiragen sama a shekarar 2020, wanda Trump ne ya ba da umarni.
Trump da kansa ya yi magana game da wannan barazana, inda ya gaya wa manema labarai cewa:
"Suna son kashe shugaban Amurka, watau ni. Ina cikin jerin sunayen da suka rubuta. Da safe na ga sunana a ko'ina. A yanzu na kubuta, amma wataƙila wannan ba zai dawwama ba. Waɗannan mutanen mugayen gaske ne, kuma dole ne a kawar da su."

Kara karanta wannan
Kotu ta umarci a tsare malamin jami'ar ABU saboda kalaman da ya yi kan gwamnatin Katsina
Daga bisani, Trump ya ƙara da cewa ya gano cewa Iran ta saka sunansa a cikin jerin waɗanda take son kashe su, duk da ba a sani ba ko yana nufin sabon rahoton Isra'ila ne.
A ƙarshen mako da ya gabata, jama'a a Iran suka rera taken "mutuwa ga Trump" a yayin jana'izar Ayatollah Ali Khamenei, Babban Jagoran Iran da aka kashe a farkon yaƙin tsakanin ƙasashen biyu.

Source: Facebook
Hakan na zuwa ne yayin da sabanin da ke tsakanin Amurka da Iran ya ƙara tsananta da kwanakin nan, bayan da ɓangarorin biyu sun kai wa juna hare-hare.
Amurka ta kai hari Iran
A wani labarin, mun kawo muku cewa rundunar sojin Amurka ta kai farmaki kan wasu wurare a Iran duk da cewa sun tsagaita wuta.
Harin ya zo ne a daidai lokacin da shugabanni da jama'ar Iran ke gudanar da jana'izar shugabansu da aka kashe, Ayatollah Ali Khamenei.
Biyo bayan lamarin, shugabannin Iran sun mayar da martani mai zafi wajen kai hare-hare a sansanonin Amurka a kasashen Gabas ta Tsakiya.
Asali: Legit.ng
