Yadda Musayar Wuta tsakanin Sojoji da Boko Haram Ya Yi Ajalin Amarya a Borno

Yadda Musayar Wuta tsakanin Sojoji da Boko Haram Ya Yi Ajalin Amarya a Borno

  • Wani mummunan harin Boko Haram ya jefa ango da sauran mazauna wani yankin jihar Borno a cikin tashin hankali bayan an rasa rai
  • Boko Haram sun kai hare-hare kan sansanonin sojoji biyu a Maiduguri da safiyar Juma'a 10 ga watan Yuli, 2026, inda aka yi asarar ran wata amarya
  • Rundunar Operation Hadin Kai ta ce ta dakile duk yunkurin kutsawar 'yan ta'addan ISWAP cikin Maiduguri, saboda haka an samu saukin barnar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno – Wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hare-hare kan sansanonin sojoji biyu da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

A yayin harin, an yi rashin sa'a inda mutane uku suka rasa rayukansu sakamakon harbin da ya biyo bayan musayar wuta tsakanin 'yan ta'addan da sojoji.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe jami'in tsaro har da sace mutane a Abuja

Boko Haram ta kai hare-hare zuwa Borno
Taswirar jihar Borno da ke fama da ta'addanci Hoto; Legit.ng
Source: Original

Daily Trust ta kawo labarin cewa cahotanni sun ce maharan sun fara kai hari kan sansanin sojoji da ke Kofa da 2.14 na dare, kafin su sake kai wani hari a sansanin da ke Muna da misalin karfe 2.30 na dare.

Boko Haram ta kai hare-hare Borno

Majiyoyi daga yankunan biyu sun shaida cewa maharan sun iso ne a kan babura suna ta harbe-harbe ba tare da sun 'dan sarara ba.

Sai dai an ce sojoji sun yi nasarar dakile dukkannin hare-haren. Duk da haka, mutum uku fararen hula sun mutu bayan harsasai sun same su yayin musayar wutar.

Wata mazauniyar Kofa mai suna Deborah Usman ta ce yayin da maharan suka fara musayar wuta da sojoji, mutane da dama sun tsere domin neman mafaka.

Ta ce wata makwabciyarsu, sabuwar amarya da ta yi makonni uku kacal da aure, ta samu gamu da tsautsayi inda harsashi ya huda mata kai, kuma ta rasu nan take.

Kara karanta wannan

Sojoji sun cafke 'yar kasar waje mai safarar miyagun kwayoyi ga 'yan ta'adda

Sojoji sun dakile harin Boko Haram

A yankin Muna kuwa, majiyoyi sun ce maharan sun yi artabu da sojojin da ke bakin ofishin Hukumar Kwastam yayin da suke kokarin kutsawa cikin birnin Maiduguri.

Sojoji sun mayar da martani ga harin yan Boko Haram
Wasu daga cikin sojojin Najeriya a bakin aiki Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Wani mazaunin yankin, Mannanaye Muhammad, ya ce mutum biyu sun mutu a lokacin harin a lokacin suna kokarin tserewa domin su tsira.

Harin ya zo ne kasa da sa'o'i 24 bayan wani hari da aka kai sansanin sojoji a garin Logomani da ke karamar hukumar Ngala, inda wani soja ya rasa ransa.

Da yake tabbatar da harin, mukaddashin jami'in yada labarai na Operation Hadin Kai, Kyaftin Mohammed Goni, ya ce dakarun rundunar sun dakile yunkurin kutsawar 'yan ta'addan ISWAP daga wurare daban-daban a jihar Borno.

Sojoji sun gwabza da yan Boko Haram

A wani labarin, kun ji cewa rahoto ya ce maharan kungiyar ya ta'addan ISWAP sun kai hari a sansanin soji da ke Logomani a karamar hukumar Ngala jihar Borno da daddare lamarin da ya jawo martani daga dakarun.

Kara karanta wannan

Sojoji sun samu gagarumar nasara bayan kashe manyan yan ta'adda 8 a Katsina

An kashe soja daya a harin, sannan mayakan sun kone ofishin 'yan sanda, asibitin kiwon lafiya da ajujuwa a makaranta yayin da dakarun suka farmaki 'yan ta'addan bayan harin, kuma an aika da ƙarin sojoji domin ƙarfafa masu.

Kyaftin Muhammed Goni, wanda ke aiki a matsayin jami'in watsa labarai na hedikwatar rundunar Operation Hadin Kai a Arewa maso Gabas, ya tabbatar da aukuwar wannan farmakin da ya jikkata sojojin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng