Wani Mutumi Ya Harba Bindiga a Gidan Gwamnatin Amurka, Trump Ya Kira Sunan Iran

Wani Mutumi Ya Harba Bindiga a Gidan Gwamnatin Amurka, Trump Ya Kira Sunan Iran

  • Shugaban Amurka Donald Trump ya tsallake rijiya da baya bayan wani harbin bindiga da ya afku a yayin da take wani taro a fadar White House
  • Maharin, mai suna Cole Tomas Allen, ya bude wuta ne a wajen dakin taron, inda jami'an tsaro suka yi gaggawar fitar da Trump
  • Duk da wannan hari, Trump ya jaddada cewa babu abin da zai dakatar da shi daga yaki da kasar Iran, wanda a halin yanzu yake fuskantar kalubale

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Amurka – Jami’an tsaro a birnin Washington sun sanar da cafke wani mutum mai shekaru 31, Cole Tomas Allen, wanda ake zargi da bude wuta a wajen taron cin abincin dare na kungiyar 'yan jaridun fadar White House (WHCA).

Shugaba Donald Trump, wanda jami'an sirri suka fitar da shi cikin gaggawa daga dakin taron, ya bayyana cewa wannan harin ba zai taba canza aniyarsa ta "cin nasara a yakin Iran" ba.

Kara karanta wannan

Bayan ta da hankalin Trump da matarsa, an gano wanda ya kai hari yayin liyafa

Donald Trump ya kira sunan Iran bayan harin da aka kai fadar White House.
Donald Trump ya na gudanar da taron manema labarai jim kadan bayan an yi harbi a White House. Hoto: Nathan Howard/Getty Images
Source: Getty Images

Trump ya kira Iran bayan hari a Amurka

Aljazeera ta rahoto cewa, a wani jawabi da ya yi wa manema labarai jim kadan bayan faruwar lamarin, Trump ya ce:

"Wannan ba zai taba dakatar da ni daga cin nasara a yakin Iran ba. Ban sani ba ko wannan harin yana da alaka da yakin, amma bisa abin da muka sani a yanzu, ban tsammanin akwai alaka ba."

Lamarin ya afuku ne a dakin taron otal din Washington Hilton, inda daruruwan 'yan jarida da baki suka buya a karkashin tebura bayan jin karar harbin bindiga.

Jami'an tsaro sun bayyana cewa Allen, wanda ya fito daga California, yana dauke da makamai da dama kafin jami'an asiri su dakatar da shi.

Jami'in tsaron Amurka ya samu rauni

Wani jami'in tsaro ya samu rauni bayan an harbe shi a rigar kariya, amma ana sa ran zai rayu.

Lauyar gwamnati Jeanine Pirro ta bayyana cewa ana tuhumar Allen da laifuka na farko da suka hada da amfani da makami da kuma kai wa jami'i hari.

Kara karanta wannan

Jami'ai sun kai wa Trump da matarsa dauki bayan ɗan bindiga ya kai hari taron White House

Ta kara da cewa za a gurfanar da shi a gaban kotun tarayya a ranar Litinin yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan ainihin dalilin da ya sa ya kai harin.

Kafin faruwar wannan hari a ranar Asabar, Trump ya soke ziyarar wakilansa zuwa Pakistan inda aka tsara gudanar da tattaunawar zaman lafiya da Iran.

An kama mutumin da ya yi harbi a wajen fadar White House, Amurka.
An kama Cole Tomas Allen, wanda ake zargi da bude wuta a wajen taron cin abincin dare na kungiyar 'yan jaridun fadar White House (WHCA). Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Trump ya tabo batun sadaukarwar shugabanci

Trump ya bayyana cewa bai gamsu da yadda Iran ke tattaunawa ba bayan kwashe kusan watanni biyu ana gwabza yaki, in ji rahoton Arab News.

Da yake magana kan hatsarin da ke tattare da shugabanci, Trump ya ce:

"Zama shugaban kasa sana'a ce mai hatsari, kuma yunkurin tada hankali a kaina wani bangare ne na aikin. Idan kana yin tasiri a duniya, dole mutane su biyo bayanka."

A waje kuwa, jirage masu saukar ungulu sun dinga shawagi yayin da dakarun tsaro na kasa suka mamaye yankin domin tabbatar da tsaro.

An soke tattaunawar Iran da Amurka

A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaba Donald Trump ya dakatar da tafiyar wakilansa zuwa birnin Islamabad, lamarin da ya soke zaman tattaunawa da Iran.

Kara karanta wannan

Babbar magana: An soke tattaunawar da aka shirya tsakanin Amurka da Iran

Shugaban kasar Amurkan ya bayyana cewa ya dauki wannan matakin ne saboda yadda ake ta kwan-gaba kwan-baya kan shirya zagaye na biyu na zaman sulhu.

Bayanai sun nuna cewa Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya bar birnin Islamabad bayan ganawa da jami'an Pakistan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com