Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Harbe Malamin Addini har Lahira a Adamawa

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Harbe Malamin Addini har Lahira a Adamawa

  • Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kar Fasto Emmanuel Ezeoikwe har lahira a gidansa da ke ƙauyen Zinal, ƙaramar hukumar Song
  • Rundunar ’yan sandan Jihar Adamawa ta tabbatar da kisan, inda ta bayyana cewa maharan sun farmaki ƙauyen ne da tsakar daren ranar Talata
  • Kwamishinan ’yan sandan jihar ya bayar da umarnin gudanar da bincike na musamman tare da tura dakarun domin kamo waɗanda suka kai harin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Adamawa – Rundunar ’yan sandan Jihar Adamawa ta tabbatar da kisan wani malamin addini, Fasto Emmanuel Ezeoikwe.

Rundunar ta sanar da cewa wasu ’yan bindiga ne suka harbe Fasto Emmanuel Ezeoikwe a ƙauyen Zinal da ke ƙaramar hukumar Song.

'Yan bindiga sun kashe fasto a Adamawa
Taswirar jihar Adamawa, inda 'yan bindiga suka kashe fasto. Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan bindiga sun kashe fasto a Adamawa

Kara karanta wannan

Hankalin iyalan mutum 416 da Boko Haram ta sace ya tashi yayin da wa'adi ya kusa cika

Wannan mummunan lamari ya faru ne a cikin daren ranar Talata, 21 ga watan Afrilu, 2026, kamar yadda rahoton jaridar Punch ya nuna.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje, ya fitar da wata sanarwa a yau Alhamis inda ya bayyana yadda harin ya faru.

SP Suleiman Nguroje ya bayyana cewa rundunar 'yan snada ta samu rahoton harin ne da misalin ƙarfe 6:30 na safiyar 21 ga Afrilu.

"A ranar 21 ga Afrilu, 2026, mun samu rahoton cewa da misalin ƙarfe 12:48 na dare, wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun shiga ƙauyen Zinal inda suka harbi faston," in ji SP Suleiman.

Binciken jami'an tsaro

SP Nguroje ya ƙara da cewa a lokacin da jami’an 'yan sanda suka isa wurin, sun tarar da Faston kwance cikin jini, inda suka garzaya da shi asibiti.

Sai dai, mai magana da yawun 'yan sandan ya ce likitoci sun tabbatar da cewa ya riga ya mutu, kamar yadda jaridar The Sun ta ruwaito.

"Lokacin da aka kai shi asibiti, likitan da ya duba shi ya tabbatar da cewa ya mutu. Yanzu haka an kai gawarsa dakin ajiye gawa na asibitin domin gudanar da bincike."

Kara karanta wannan

Majalisa ta dauki mataki kan hare haren Boko Haram da suk kashe manyan sojojin Najeriya

- SP Suleiman Nguroje

Rundunar 'yan sanda ta fara gudanar da bincike domin gano 'yan bindigar da suka kashe fasto a Adamawa.
Wasu jami'an rundunar 'yan sanda dake aikin sintiri lokacin zabe. Hoto: @Princemoye1
Source: Twitter

'Yan sanda sun yi kira ga jama'a

Jami'an tsaro sun samu kwankon harsasan bindiga ƙirar AK-47 guda uku a wurin da abin ya faru, wanda hakan ke nuna irin haɗarin makaman da maharan suka yi amfani da su.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Kabir Hassan, ya bayar da umarnin gudanar da bincike na sirri tare da baza dakarun yaki da makamai domin bin sawun waɗanda suka aikata wannan danyen aiki.

Rundunar ta yi kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankulansu tare da bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen kamo maharan.

'Yan bindiga sun kashe matar fasto

A wani labari, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kashe matar fasto na cocin Anglican a lokacin da suka farmaki cocin Saint Andrew da ke a kauyen Isiokwe.

Legit Hausa ta fahimci cewa, kauyen Isiokwe ya na cikin gundumar Lilu, karkashin karamar hukumar Ihiala da ke jihar Anambra, Kudu maso Gabashin Najeriya.

A wani bidiyo da ya bazu, an ga yadda gidan faston ya kone kurmus, sannan an ga motoci biyu da wani babur duk sun gama cinye wa da wuta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com