Hukumar EFCC
A shekarar 2020, hukuma ta dakatar da wasu manyan jami’ai saboda binciken Tinubu, Atiku wanda ake ganin su na harin fitowa takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa
Za ku ji yadda Tanimu Turaki ya karkatar da kudin Gwamnati zuwa asusun jama’a. Wani jami’in EFCC ya ce sun gano N75m a asusun Mai dakin tsohon Ministan kasar.
Wata kotu dake zaune a Ilori, birnin jihar Kwara, ya yankewa wani direba, Adetunji Tunde, hukuncin shekaru biyu a gidan kaso kan amfani da kudin da ba nashi ba.
Za ku ji cewa wani ya kai karar Shugaban hukumar zabe na kasa gaban Kotu a Najeriya. Hon. Emmanuel Agonsi shi ne ya shigar da wannan kara mai lamba a Abuja.
EFCC ta koma gaban Alkali da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal. Ana zargin Injiniya Babachir David Lawal da satar Naira miliyan 544.
Wani shaidan da EFCC ta kira a kotu ya tona badakalar da aka yi a baya inda Kamfanoni da ‘Yan Majalisa su ka rika raba ribar da aka samu kwangilolin mazabu.
Tsohon shugaban kwastan na Njeriya da tsohon Akanta-Janar na Tarayya sun mayar da kudin da a ke zargin sun yi sama da fadi dashi asususn gwamnatin tarayya.
A 2020, Alkalai sun daure mutane 800 a cikin kara 1300 da EFCC ta kai Kotu. Hukumar EFCC ta gurfanar da mutane 1300 a gaban kotu a shekarar nan da za ta fita.
A cikin 2010 Ma’aikatar tsaro ta bada kwangilar N960m, kuma ta fitar da kudin babu amincewar FEC. Majalisa ta bankado badakalar nan bayan shekaru kusan biyar.
Hukumar EFCC
Samu kari