EFCC ta damke wasu daliban makarantar damfara a Abuja

EFCC ta damke wasu daliban makarantar damfara a Abuja

- EFCC ta samu nasarar damke daliban makarantar koyar da damfara a babban birnin tarayya Abuja

- An kama matasan daliban da abubuwan aikata laifi daban-daban a hannunsu

- Sai dai malamin nasu ba a samu nasarar kame shi ba, an bayyana ya cika wandonsa da iska

Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC) a ranar Juma'a ta cafke wasu mutane 10 da ake zargi da damfara ta hanyar kwamfuta da ake kira 'Yahoo-Yahoo'

An kama su ne a makarantar su ta Bwari da ke Abuja inda aka ce suna koyon sana'ar yaudarar mutane, Daily Nigerian ta ruwaito.

Wadanda ake zargin masu shekaru tsakanin 20 zuwa 30, su ne Sixtus Jude, Moses Samuel, Isalan Johnny, Dapet Nimshak, Samuel Ogboche, Victor Samuel, Victor Asuquo, Ibrahim Yunusa, Yahaya Usman da Chijoke Ikwuoha.

KU KARANTA: An sace tawagar abokan ango a jihar Taraba

EFCC ta damke wasu daliban makarantar damfara a Abuja
EFCC ta damke wasu daliban makarantar damfara a Abuja Hoto: P.M News
Asali: UGC

An kama su tare da abubuwa daban-daban na laifi kamar wayoyin hannu da kwamfutoci.

Mai tallata makarantar kwalejin tuni ya gudu.

Bincike ya nuna cewa wadanda suka dauki nauyin makarantar sun horas da matasa wadanda suka nuna sha'awarsu ga yaudarar mutane ta yanar gizo.

Mai daukar nauyin yana samun kaso na kudaden da yake samu bisa yarjejeniya tsakanin sa da wadanda aka dauka. Hakanan ya kasance shine hanya safarar kudaden da wasu daga cikin wadanda ake zargin suka damfara ta hanyar yanar gizo.

Za a gurfanar da wadanda ake zargin a lokacin da aka kammala bincike.

KU KARANTA: COVID-19 ta shiga jerin kalubalen duniya kamar ta'addanci, rashawa, in ji Buhari

A wani labarin, Sojojin Najeriya tare da goyon bayan kungiyar hadin gwiwa ta Multinational Joint Taskforce, MNJTF, sun mamaye wasu yankuna hudu na Boko Haram a Arewa maso Gabas.

An bayyana nasarar ne 'yan sa'o'i bayan sanarwar sabbin hafsoshin soja.

Aikin da Brig. Gen Waidi Shaibu, Birgediya kwamandan runduna ta musamman ta 21, ya afkawa mayakan Boko Haram da dama a Maiyanki, Darulsallam, Bula Kurege da Izza.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel