CCB, Hukumar INEC za su je kotu a kan kadarorin Mahmoud Yakubu

CCB, Hukumar INEC za su je kotu a kan kadarorin Mahmoud Yakubu

- Wani mutumi ya kai karar Shugaban INEC, Mahmoud Yakubu a kotu

- Emmanuel Agonsi yana son ganin takardun kadarorin Farfesa Yakubu

- Yakubu ya yi shekara 5 a INEC, kuma ya taba rike shugaban TETFund

An kai karar shugaban hukumar INEC mai gudanar da zabe a Najeriya, Farfesa Mahmoud Yakubu, gaban wani babban kotun tarayya a Abuja.

Jaridar Leadership ta ce an hada da hukumar CCB mai tantance kadarorin ma’aikata da jami’an gwamnatin Najeriya a wannan kara da aka kai.

Hon. Emmanuel Agonsi shi ne ya shigar da wannan kara mai lamba FHC/ABJ/CS/33/2021 ta hannun lauyansa, Barista E. C. Muokwudo.

Barista E. C. Muokwudo ya na neman kotu ta ba hukumar CCB umarni a fito da takardun mallakar kadarorin shugaban INEC, Mahmoud Yakubu.

KU KARANTA: Yakubu zai mikawa wani ragamar INEC, wa'adinsa ya kare

Bayan haka wannan lauya ya roki Alkali ya tursasa CCB ta fito da takardun da ke bayanin kadarorin ‘ya ‘yan Yakubu da ke zama a karkashinsa.

Har ila yau, wannan Lauyan ya na son ganin takardun kadarorin Mahmoud Yakubu na shekarar 2007 zuwa 2012, da shekarar 2015 zuwa 2020.

A ranar 20 ga watan Disamba, 2020, Lauyan da ya tsaya wa Agonsi ya rubuta takarda zuwa ofishin CCB ya na neman bayanan shugaban INEC.

A takardar, Emmanuel Agonsi ya bayyana kansa a matsayin kungiyarsa ta na yaki da rashin gaskiya a cikin ma’aikatan gwamnati a Najeriya.

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya na gina gidan yari a Abuja

CCB, Shugaban INEC za su je kotu a kan kadarorin Mahmoud Yakubu
Farfesa Mahmoud Yakubu Hoto: Twitter Daga: @INECNigeria
Asali: Twitter

Agonsi ya dogara da sashen farko na dokar FoI na shekarar 2011, ya bukaci a bashi fam din Mahmoud Yakubu da ‘ya ‘yansa da ba su yi aure ba.

Farfesa Mahmoud Yakubu ya rike hukumar TETFund, daga baya ya zama shuugaban INEC.

A makon nan ne shaidan farko da hukumar EFCC ta kawo yayi magana a karar tsohon SGF, Babachir Lawal inda ake zarginsa da satar N544m.

An fara gabatar da wadanda ake tuhuma ne a wani babban kotun tarayya na Abuja a ranar 30 ga watan Nuwamba, 2020, sai Alkalin kotun ya mutu.

Wani Alkali ya cigaba da sauraron zargin satar dake kan tsohon sakataren gwamnatin tarayyar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng