Mun karbi korafi 10000, mun binciki 7300, an kai 1300 kotu inji Hukumar EFCC
- Shugaban EFCC ya ambaci irin nasarorin da su ka samu a wannan shekarar
- Mohammed Umar Abba ya ce EFCC ta yi sanadiyyar daure mutane har 800
- A haka don ma annobar Coronavirus ta sa abubuwa sun ja baya sosai a bana
Mukaddashin shugaban hukumar EFCC na kasa, Mohammed Umar Abba, ya ce sun yi nasarar daure mutane 865 daga kara 1, 305 da su ka kai kotu.
Jaridar Punch ta rahoto EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ta na cewa sun binciki zargi 7, 340 daga cikin korafi 10, 152 da su ka samu a shekarar nan.
A jiya shugaban EFCC, Mohammed Umar Abba ya fitar da jawabin karshen shekara ne ta bakin mai magana da yawun hukumar, Wilson Uwujaren.
Mista Wilson Uwujaren ya bayyana cewa sabon shugaban rikon kwayar ya godewa jami’an hukumar da irin kokarin da su ka nuna wajen samun wannan nasara a 2020.
KU KARANTA: Buhari zai bayyana EFCC da ICPC
A cewar Mohammed Umar, shekarar 2020 ta fita dabam ganin yadda annobar COVID-19 ta yi tasiri a aikinsu.
“Takunkumin da aka kakaba domin rage yaduwar cutar COVID-19 ya haddasa raguwar aikinmu. An yi fiye da watanni biyar, abubuwa sun yi kasan da ba su taba yi ba a shekaru 17 da mu ka yi”
Jawabin na Wilson Uwujaren ya kara da cewa cire shugaban hukumar da aka yi a yunkurin gyaran da ake yi a EFCC, ya taimaka wajen rage kwarin gwiwan ma’aikata.
Amma duk da haka, EFCC ta dace da nasarori da-dama a bakin aiki, da su ka hada da daure mutane 800 da aka samu da laifi.
KU KARANTA: David Mark ne silar nasarar tashi na a siyasa – Gwamnan Bauchi
Abba ya bayyana kokarin da su ke yi na hada-kai da sauran jami’an tsaro, tare da inganta yadda ake tafiyar da aiki. A karshe ya yi wa ma’aikata alkawarin za a kula da jin dadinsu.
“Idan EFCC ta gaza, an gaza yaki da rashin gaskiya a Najeriya.” Abba ya fadawa jami’ansa.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng