Abdulaziz Yari ya bayyana a ofishin EFCC na Legas, ya sha dogayen tambayoyi
- Hukumar EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari
- Abdulaziz Yari ya shafe sa’o’i a babban ofishin EFCC a Garin Legas a jiya
- Ana zargin yunkurin fitar da kudi ya sa EFCC ta gayyaci Yari ya yi bayani
Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, ya dauki sa’o’i a ranar Talata, 2 ga watan Fubrairu, 2021, a hannun jami’an hukumar EFCC.
Jaridar Premium Times ta samu rahoto cewa an ga tsohon gwamnan a ofishin EFCC da ke titin Awolowo, Ikoyi, jihar Legas da kimanin karfe 11:00 na safe.
Alhaji Abdulaziz Yari ya hallara ofishin EFCC ne domin amsa goron gayyatar da aka aika masa.
Majiyar jaridar ta bayyana cewa Abdulaziz Yari ya fada hannun EFCC ne bayan ya yi yunkurin karkatar da Naira biliyan 300 daga asusun wani kamfani.
KU KARANTA: Zamfara: Dunkulewar APC ba ta da tasiri a wurinmu - PDP
Kawo yanzu jaridar ba ta samu cikakken labarin abin da ya wakana ba, amma kokarin ‘dan siyasar na zarar wannan kudi ta wani banki bai iya yiwuwa ba.
Da ya shiga hannun EFCC, tsohon shugaban gwamnonin na Najeriya ya ba hukumar EFCC dogon jawabi, daga baya aka sallame shi da maraicen ranar Talatar.
Ta tabbata cewa Abdulaziz Yari ya bar ofishin hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa a jiya, har ya yi waya da mutane.
Amma alamu na nuna cewa akwai yiwuwar a sake kiran tsohon gwamnan, kuma daya daga cikin kusoshin jam’iyyar APC domin ya amsa wasu tambayoyin.
KU KARANTA: An sulhunta Yari da Sanata Marafa a Zamfara
Da aka tuntubi mai magana da yawun bakin EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar da cewa Yari ya ziyarci ofishinsu, amma bai yi karin bayani kan lamarin ba.
A makon jiya ne tsohon Gwamnan Zamfara, AlhajiAbdulaziz Abubakar Yari ya fito ya yi magana bayan Alkali ya bada umarni a karbe masa tulin dukiyarsa.
Abdulaziz Yari ya ce kudinsa za su dawo domin kuwa an bada dama ya kare kan shi a kotu.
Abdulaziz Yari ya yi magana ne ta bakin mai magana da yawun bakinsa, Mayowa Oluwabiyi, a ranar Lahadi, ya na mai yi karin haske game da hukuncin kotun.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng