Abdulaziz Yari ya ce zai daukaka kara a shari’ar $669, 248 da N24.3m da Gwamnati

Abdulaziz Yari ya ce zai daukaka kara a shari’ar $669, 248 da N24.3m da Gwamnati

- Abdulaziz Yari ya ce Lauyoyinsa za su daukaka kara a shari’arsa da ICPC

- Kwanakin baya kotu ta bada umarnin a karbe wasu tarin kudi da ya mallaka

- Yari ya ce an bada kwanaki 14 ya kare kansa, kafin kudin su bar hannunsa

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, ya yi watsi da rahotannin da ke cewa kudinsa $669,248 da N24.3m sun koma hannun gwamnatin tarayya.

Jaridar Daily Trust ta ce Abdulaziz Yari ya yi magana ta bakin mai magana da yawun bakinsa, Mayowa Oluwabiyi, a ranar Lahadi, 31 ga watan Junairu, 2021.

Mayowa Oluwabiyi ya ce duk da Alkali mai shari’a, Ijeoma Ojukwu, ta bada umarni gwamnatin tarayya ta rike dukiyar mai gidansa, kotu ta ba shi kofa.

Oluwabiyi ya ce Ijeoma Ojukwu ta ba tsohon gwamnan kwanaki 14 domin ya yi wa kotu bayani mai gamsar wa da zai hana a karbe masa wadannan kudi.

KU KARANTA: EFCC ta kai farmaki gidan tsohon gwamnan Zamfara, Yari

A cewar Mayowa Oluwabiyi, tsohon gwamnan na Zamfara ya fara shirin daukaka shari’a a babban kotun daukaka kara, ya na kalubalantar hukuncin da aka yi.

Jawabin ya ce, Abdul’aziz Abubakar Yari, bai jin tsoron komai domin ya tabbatar da duk kamfanoni da kasuwancin da ya mallaka a gaban CCB.

Abdul’aziz Yari ya kuma bayyana cewa CCB ta tabbatar da kadarorin na sa bayan ya zama gwamna. Yari ya yi mulki a jihar Zamfara tsakanin 2011 da 2019.

Jagoran na APC ya yi kira ga jama’a su jira a karkare shari’a kafin su zartar masa da hukunci.

KU KARANTA: An zargi Yari da saba dokar COVID-19 a filin jirgi

Abdulaziz Yari ya ce zai daukaka kara a shari’ar $669, 248 da N24.3m da Gwamnati
Abdulaziz Yari Hoto: www.vanguardngr.com
Asali: UGC

Yari ya ce ya na sa ran Alkalan kotun da za a je za su dawo masa da kudinsa wanda adadinsu ya haura Naira miliyan 260 idan aka yi la’akari da farashin Dala.

A ranar Litinin, 25 ga watan Junairu, 2021, kun ji cewa gwamnatin jihar Imo ta fito ta na zargin tsohon gwamna, Sanata Rochas Owelle Okorocha da laifin sata.

Gwamnan Hope Uzodinma ya ce ba a taba mummunar gwamnati a Imo kamar ta Okorocha ba.

Kwamishinan yada labarai da dabaru, Declan Emelumba, ya ce tsohon gwamnan ya yi facaka da baitul-mali, don haka ne ma yanzu yake hanyar zuwa kurkuku.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel