Wasu kungiyoyi sun nemi Buhari ya saki rahoton kwamiti game da Magu

Wasu kungiyoyi sun nemi Buhari ya saki rahoton kwamiti game da Magu

- Wasu kungiyoyi sun bukaci shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana gaskiyar lamarin Magu

- Kungiyoyin sun roki Buhari ya fdda rahoton kwamitin da aka kafa don bincike kan Magu

- Kungiyoyin sun bayyana cewa, lamarin Magu ne ya jawo faduwar Najeriya a shirin Transparency International

An bukaci Shugaba Muhammadu Buhari da ya gabatar da rahoton kwamitin shari’a kan tsohon Mukaddashin Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu, Premium Times ta ruwaito.

A cikin wata wasika da aka aika wa shugaban, babbar kungiyar kawancen yaki da cin hanci da rashawa ta duniya ta nuna matukar damuwar cewa an tsoma bakin siyasa a cikin aikin EFCC.

Ta kuma bayyana gazawar mahukuntan Najeriya wajen fitar da rahoton dake da alhakin faduwar Najeriya a kwanan nan a shirin yaki da cin hanci da rashawa da kungiyar Transparency International ta yi.

KU KARANTA: COVID-19: Jihohi 7 a arewacin Najeriya za su mori tallafin $900,000

Wasu kungiyoyi sun nemi Buhari ya saki rahoton kwamiti game da Magu
Wasu kungiyoyi sun nemi Buhari ya saki rahoton kwamiti game da Magu Hoto: BBC World
Source: UGC

Kungiyoyin, HEDA Resource Center, Global Witness, Re: Common da kuma The Corner House, sun ce gazawar gwamnatin tarayya na fitar da rahoton ya nuna cewa duk aikin farautar mayu ne.

Olanrewaju Suraju, Simon Taylor, Luca Manes da Nicholas Hildyard ne suka sanya hannu a takardar.

Gamayyar kungiyar ta ce ba ta da wata shakku a kan cewa, sai dai idan an hanzarta warware matsalar, harkallar da Babban Lauyan Tarayya, Abubakar Malami, ya yi a kan Mista Magu na iya zama wani abin sha'awa.

Kungiyar ta ce "Saboda Najeriya da kuma martabar shugabancin ka, ba tare da wata shakka ba muna roƙon ka da ka yi la’akari da ganin cewa ba yin adalci kawai ba, ya kamata za a ga an aikata adalci a cikin lamarin”.

KU KARANTA: An ceto wasu daga matasan takum 25 da aka sace

A wani labarin, Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC) a ranar Juma'a ta cafke wasu mutane 10 da ake zargi da damfara ta hanyar kwamfuta da ake kira 'Yahoo-Yahoo'.

An kama su ne a makarantar su ta Bwari da ke Abuja inda aka ce suna koyon sana'ar yaudarar mutane, Daily Nigerian ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel