Tsohon shugaban kwastam da wani sun mayar da N8bn asusun gwamnati

Tsohon shugaban kwastam da wani sun mayar da N8bn asusun gwamnati

Wasu manyan jiga-jigan gwamnatin tarayya sun mayar da kudaden da a ke zargin sun yi sama da fadi dasu

- Daya daga ciki ya kasance tshohon Akanta-Janar na Tarayya, Jonah Ogunniyi Otunla

- Daya kuwa ya kasance tsohon kwanturola na kwastom, Andullahi Inde Dikko

Wani tsohon Akanta-Janar na Tarayya (AG-F), Jonah Ogunniyi Otunla, da wani tsohon Kwanturola-Janar na Kwastam, Abdullahi Inde Dikko, sun mayar da Naira biliyan 6.3 da biliyan N1.9, The Nation ta ruwaito.

Otunla shi ne AG-F tsakanin 2011 da 2015 yayin da Dikko ya kasance Kwanturola Janar na Kwastam tsakanin 2009 da 2015.

Yayin da Otunla ya dawo da N6,392,000,000.00; Dikko ya dawo da N1,596,000,000.00 (daidai da $8m, wanda aka kirga kan N197 zuwa dala Amurka kan farashin canjin da ake yi a lokacin).

KU KARANTA: Jihar Ekiti zata kashe N1.4bn Domin karfafa 'yan bangan Amotekun

Tsohon shugaban kwastam da wani sun mayar da N8bn asusun gwamnati
Tsohon shugaban kwastam da wani sun mayar da N8bn asusun gwamnati Hoto: The Nation/The Guardian
Asali: Depositphotos

Ya bayyana cewa wani lokaci a cikin shekarar 2015, kungiyar masu binciken EFCC ta gayyace shi, inda suka binciki zargin karkatar da kudaden daga Ofishin Mai Bayar da Shawara Kan Harkokin Tsaro (ONSA) da kuma kudaden fansho na Kamfanin Holding Power of Nigeria (PHCN).

Otunla ya ce ya hadu da Magu a yayin gudanar da bincike, lokacin da mukaddashin shugaban hukumar EFCC na wancan lokacin ya ce masa "ka mayar da kudaden da ke da alaka da kamfanonin ka babu wanda zai tuhume ka."

Dangane da yarjejeniyar, Otunla ya ce daya daga cikin kamfanonin da ke da nasaba da shi - Stellar Vera Development Ltd - ya mayar da N750m; wani kamfanin - Damaris Mode Coolture Ltd - ya dawo da N550m.

Daga baya kamfanonin biyu suka kara biyan hadin gwiwa na N2, 150,000,000.00.

Dikko, ya ce ya kulla yarjejeniya da Babban Lauyan Tarayya (AGF) da Ministan Shari'a, Abubakar Malami "don mayar da $8m ko kwatankwacin ta a kan naira a N197 zuwa dala.

KU KARANTA: An samu mai dauke da cutar Korona a magarkamar 'yan sanda

Dikko ya bayyana, a daya daga cikin takardun kotun, cewa jim kadan bayan ya yi ritaya, ya shiga wata yarjejeniya a ranar 25 ga Mayu, 2016 tare da AGF da Darakta Janar na Hukumar Tsaron Jiha.

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya musamman manyan mutane da su yi adalci wajen sukar gwamnatinsa ta hanyar duba halin da kasar ke ciki kafin hawan gwamnatin yanzu, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaba Buhari ya yi wannan kiran ne a ranar Alhamis a fadar gwamnati da ke Abuja, yayin da ya karbi bakuncin Reverend Yakubu Pam, Sakatare Janar na Hukumar Alhazai ta Kiristocin Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.