An Kai Hari Gidan Fitaccen Ɗan Kwallo bayan Sifaniya Ta Doke Faransa a Kofin Duniya

An Kai Hari Gidan Fitaccen Ɗan Kwallo bayan Sifaniya Ta Doke Faransa a Kofin Duniya

  • Wasu ɓarayi sun yi kai hari tare da yunƙurin shiga gidan Lamine Yamal, jim kaɗan bayan ƙasarsa ta kai wasan ƙarshe na Kofin Duniya 2026
  • Jami'an tsaro ne suka fara ankara da waɗanda ake zargin suna ƙoƙarin shiga gidan, lamarin da ya sa miyagun suka tsere kafin isowar 'yan sanda
  • 'Yan sandan Catalonia sun fara bincike kan lamarin, yayin da Spain ke ci gaba da shirye-shiryen buga wasan ƙarshe na gasar cin Kofin Duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Barcelona -Wasu mutane da ake zargin ɓarayi ne sun kai hari tare da yunƙurin shiga gidan tauraron ƙwallon ƙafar Sifaniya, Lamine Yamal.

Miyagun sun farmaki gidan dan wasan ne da ke Barcelona, jim kaɗan bayan Yamal ya taimaka wa ƙasarsa ta kai wasan ƙarshe na gasar cin Kofin Duniya ta 2026.

Kara karanta wannan

Kofin Duniya: An hango abin da zai iya kawo cikas ga wasan Ingila da Argentina

Barayi sun yi yunkurin balle gidan tauraron kwallon kafa, Lamine Yamal
Lamine Yamal #19 na Sifaniya yana magana da manema labarai a filin wasan Dallas a ranar 13 ga Yuli, 2026. Hoto: Hector Vivas - FIFA/FIFA via Getty Images
Source: Getty Images

Jami'an tsaro sun tarwatsa ɓarayin

Rahoton Aljazeera ya nuna cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Laraba, bayan Spain ta doke Faransa da ci 2-0 a wasan dab da na ƙarshe da aka buga a Texas.

'Yan sandan yankin Catalonia sun tabbatar da cewa an yi yunƙurin shiga wani gida a Esplugues de Llobregat da ke wajen birnin Barcelona.

Sai dai ba su bayyana sunan mai gidan ba saboda dokokin kare sirri. Duk da haka, jaridar La Vanguardia ta ruwaito cewa gidan na ɗan wasan Barcelona ne.

Rahoton ya ce mutane biyu sanye da hular ɓoye fuska sun hau katangar gidan, amma jami'an tsaro masu zaman kansu sun gano su, lamarin da ya sa suka tsere kafin isowar 'yan sanda.

Gidajen 'yan ƙwallo na fuskantar barazana

Jami'an tsaro sun fara bincike domin gano waɗanda suka yi yunƙurin shiga gidan, kamar yadda rahoton Yahoo News ya nuna.

Kara karanta wannan

Kasurgumin dan ta'addan ISIS ya shigo Najeriya, sojoji sun yi caraf da shi

Masana na duba bidiyon kyamarorin tsaron gidan domin gano bayanan da za su taimaka wajen cafke waɗanda ake zargi.

Rahotanni sun nuna cewa ba gidan Yamal kaɗai aka yi yunƙurin shiga ba, domin wasu gidaje a yankin sun fuskanci irin wannan matsala a watannin baya.

An ce ƙungiyoyin ɓarayi kan kai hari gidajen fitattun 'yan ƙwallo saboda tsadar kayan ado, agogo da sauran kayayyakin alatu da ake zargin suna ajiye wa.

Yayin da aka yi yunkurin shiga gidan Yamal, kasarsa ta Spain na shirin fafata wasan karshe da Argentina.
Lamine Yamal (Sifaniya) yayin wasan dab da na karshe na kofin duniya tsakanin Faransa da Sifaniya. Hoto: Ulrik Pedersen/NurPhoto via Getty Images
Source: Getty Images

Gidan ya taɓa zama mallakin Piqué da Shakira

Rahotanni sun ce gidan da ake magana a kai ya taɓa kasancewa mallakin tsohon tauraron Barcelona, Gerard Piqué, da tsohuwar abokiyar zamansa, mawaƙiya Shakira.

Lamine Yamal ya nuna hotunan gidan a shafukan sada zumunta kafin ya tafi gasar cin Kofin Duniya da ake yi a Amurka, Kanada da Mexico.

Yayin da ake ci gaba da bincike kan yunƙurin satar, Yamal na ci gaba da shirin buga wasan ƙarshe na gasar cin Kofin Duniya.

Sifaniya ta cire Faransa a Kofin Duniya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sifaniya ta samu nasarar doke Faransa a birnin Dallas, inda Kylian Mbappé da abokan wasansa suka kasa hana La Roja samun gurbin zuwa wasan ƙarshe.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta gwangwaje iyalan dan sandan da ya mutu a bakin aiki

Wannan ne karo na biyu a tarihin Sifaniya da ta samu damar buga wasan ƙarshe na gasar Kofin Duniya.

A halin yanzu, Sifaniya za ta kara da Argentina a wasan karshe, bayan tawagar Lionel Messi ta doke Ingila da ci 2-1 a wasan da suka fafata ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com