Manyan Zarge Zargen Almundahanar Kudi 5 da Suka Girgiza Kamfanin NNPC

Manyan Zarge Zargen Almundahanar Kudi 5 da Suka Girgiza Kamfanin NNPC

  • Kamfanin mai na kasa, NNPC ya dade yana fuskantar zarge-zargen almundahanar kuɗi da rashin bayyana gaskiya kan harkokin man fetur
  • Wasu daga cikin manyan shari'o'in sun haɗa da zargin ɓacewar kuɗaɗen mai, tallafin fetur da kuma kuɗaɗen gyaran matatun mai
  • Majalisar Dattawa ta bai wa NNPC wa'adin mako guda kan bayanin Naira tiriliyan 210 da ake cece-kuce domin a gano yadda aka haihu a rawaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Ana ci gaba da cece-kuce kan binciken kuɗin Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL), bayan kwamitin kula da asusun gwamnati na Majalisar Dattawa ya nemi cikakken bayani.

Majalusa ta nemi kamfanin ya gabatar da cikakken bayani kan wasu kuɗaɗe da suka kai Naira tiriliyan 210 da ake zargin ba a yi musu cikakken bayani ba.

Kara karanta wannan

An yi kicibis, sojoji sun yi ram da 'dan bindiga a hanyar sintiri

Ana zargin NNPCL da kartatar da kudi
Shugaban kamfanin mai na NNPCL, Bayo Ojulari Hoto; NNPC Limited
Source: UGC

BBC Hausa ta wallafa cewa lamarin ya sake jawo hankalin jama'a kan wasu manyan zarge-zargen badaƙalar kuɗi da kamfanin ya fuskanta cikin shekaru da suka gabata.

Manyan zarge-zargen da ake yi wa NNPCL

Ana yi wa kamfanin NNPCL zarge-zarge da dama da suka hada da bacewar kudi sama ko dakasa da kuma wasu kudi da ba a saka a asusun gwamanti ba.

Wasu daga cikin sun hada da:

1. Bacewar Dala biliyan 20

Jaridar Punch ta wallafa cewa a shekarar 2013, tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Sanusi Lamido Sanusi, ya yi ikirarin cewa kimanin Dala biliyan 20 daga kudIn sayar da danyen mai ba su shiga asusun gwamnati ba.

Zargin ya haifar da bincike mai fadi tare da muhawara a fadin kasar, duk da cewa gwamnati ta ce an yi bayanin wasu daga cikin kudaden.

2. Rikicin tallafin man fetur

The Sun Nigeria ta wallafa cewa binciken Majalisar Wakilai a shekarar 2012 ya bankado zargin cewa an biya biliyoyin Nairori a matsayin tallafin fetur ba bisa ka'ida ba.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: INEC na shirin yin zaben gwaji kafin siyasar 2027 a Najeriya

Rahoton ya yi nuni da cewa wasu kamfanoni sun karbi kudade ba tare da shigo da adadin man da aka bayyana ba lamarin da ya jawo cece-kuce.

3. Karkatar da kudin gyara matatu

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa kamfanin mai na NNPCL ya sha fuskantar suka kan dimbin kudaden da ake kashewa wajen gyaran matatun mai, duk da cewa matatun sun dade ba sa aiki yadda ya kamata.

Zarge zarge akalla biyar da suka danganci kudi sun dabaibaye NNPCL
Bayo Ojulari, magajin Mele Kyari a NNPCL Hoto: NNPC Limited
Source: Facebook

Masana da kungiyoyin farar hula sun dinga tambayar dalilin ci gaba da kashe makudan kudade ba tare da ganin gagarumin sakamako ba.

4. 'Kin sanya kudi a asusu

A lokuta daban-daban, masu sa ido kan harkokin gwamnati sun zargi kamfanin da rashin bayyana cikakkun bayanan kudaden shiga da kashe-kashe, lamarin da ya janyo kiraye-kirayen a kara tabbatar da gaskiya da rikon amana.

Premium Times ta wallafa cewa Kwamitin Kula da Asusun Jama'a na Majalisar Wakilai (PAC) ya umarci Ofishin Babban Akawun Tarayya (OAGF) da ya gabatar da cikakkun bayanai game da wasu kudaden shiga.

Wannan ya danganci zargin Babban Bankin Najeriya (CBN), Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL), da sauran hukumomin da ke samar da kudaden shiga da gwamnati ke binsu

Kara karanta wannan

Jigo a Jam'iyyar APC ya ruga Amurka roko wa Najeriya iri

5. Binciken Naira tiriliyan 210

Sabon batu da ya fi daukar hankali shi ne binciken da Majalisar Dattawa ke yi kan Naira tiriliyan 210 da ake zargin bayanansu ba su fito fili ba a cikin kundin bayanan kuɗin kamfanin.

Kwamitin kula da asusun gwamnati na majalisar ya bai wa NNPC wa'adin mako guda ya gabatar da takardu da za su fayyace yadda aka tafiyar da kudaden.

Sai dai jaridar Vanguard a safiyar nan ta ruwaito cewa Babban Manajan Rukunin Kamfanin Kula da Zuba Jari a Fannin Man Fetur na Kasa (NAPIMS), Bala Wunti, ya bayyana cewa akwai shakku a zargin.

Ya ce babu wata shaida a cikin bayanan kudi na shekarar 2023 da aka tantance na Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL) da ke tabbatar da ikirarin cewa Naira tiriliyan 210 sun bace daga asusun kamfanin.

Zargin NNPCL kan Dangote

A baya, mun wallafa cewa kamfanin mai na Najeriya, NNPCL ya zargi matatar Dangote da kokarin mallake kasuwar mai ta Najeriya ita kadai ba tare da barin wasu su samu dama ba.

Kara karanta wannan

Sojoji sun rikata 'yan Boko Haram a kananan hukumomin Borno 5

Kamfanin ya ce dakatar da lasisin shigo da mai zai iya haddasa karancin mai da tashin farashi a kasar nan yayin da Dangote ya maka shi a gaban kotu domin dakatatar da manufar.

Rikicin shari’ar na zuwa ne gabanin shirin matatar Dangote na sayar da hannun jari a watan Satumba, 2026 domin kara habaka samar da fetur a Afrika yayin da ake fadada ayyukan matatarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng