NFIU ta dakatar da manyan jami’ai saboda binciken Bola Tinubu, Atiku Abubakar
- An dakatar da wasu jami’ai a NFIU da su ka kirkiro binciken su Bola Tinubu
- Haka zalika wadannan ma’aikata biyu sun shiga binciken Atiku Abubakar
- Da alamu ‘yan siyasan na harin takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023
Wasu mataimakan darektoci da ke aiki a hukumar NFIU mai bincike ta kasa sun samu kansu a matsala a dalilin binciken Atiku Abubakar da Bola Ahmed Tinubu.
Jaridar Premium Times ta fitar da rahoto na musamman cewa an dakatar da wadannan jami’ai; Mohammed Mustapha da Fehintola Salisu daga bakin aikinsu a 2020.
Takardun da jaridar ta samu sun nuna an dakatar da wadannan ma’aikata da ke kula da bincike da nazari a ma’aikatar NFIU ne saboda taba manyan ‘yan siyasar.
An dakatar da Mohammed Mustapha da abokin aikinsa, Fehintola Salisu ne a Agustan 2020, bayan sun fara gudanar da bincike kan Atiku Abubakar da Bola Tinubu.
KU KARANTA: Bikin 'Yar Ribadu da Atiku ya samu halartar Tinubu da manyan 'yan siyasa
Darektan NFIU, Modibbo Tukur wanda aka nada a farkon 2019, ya rubuta takarda a ranar 13 ga watan Junairun 2021, ya na tuhumar wadannan ma’aikata biyu.
Modibbo Tukur ya zargi mataimakan darektocin da fara binciken wadannan ‘yan siyasa da ake ganin su na harin zaben 2023, ba tare da sun tuntubi ofishinsa ba.
Darektan sabuwar hukumar, Malam Tukur, ya bayyana cewa an dakatar da wadannan manyan ma’aikata ne saboda a guji wuce gona da irin da su ke aikata wa.
Mohammed Mustapha da Fehintola Salisu su na cikin tsofaffin ma’aikatan da aka kafa NFIU da su.
KU KARANTA: Wike ya fadawa Hafsun Sojoji abin da za su yi domin su samu nasara
“An samu wadannan ma’aikata biyu da yin abin da ya saba wa ra’ayin ofishinsu, domin sun yi rashin kunya da kuma kin biyayya ga hukuma mai iko.” Inji Tukur.
Tukur ya yi wannan bayani ne a matsayin martani ga takardar korafin da aka aiko wa hukumar ICPC.
Tsohon Gwamnan Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya ce jam'iyyarsu ta PDP mai hamayya za ta dawo ta karbe mulki daga hannun gwamnatin APC a zabe mai zuwa na 2023.
Da yake jawabi jiya a Kano, babban ‘Dan siyasar kuma daya daga cikin jiga-jigan adawa a Arewacin Najeriya ya hango rushewar jam’iyyar APC kafin shekarar 2023.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng