Kurunkus: Kotu Ta Yi Hukunci kan Takarar Atiku Abubakar a Zaben Shugaban Kasa na 2027

Kurunkus: Kotu Ta Yi Hukunci kan Takarar Atiku Abubakar a Zaben Shugaban Kasa na 2027

  • Babbar Kotun Tarayya da ke zama Abuja ta yi watsi da karar tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi kan takarar Atiku Abubakar a ADC
  • Lauyan Amaechi ya ce bangarorin sun sasanta sabanin da ke tsakaninsu, don haka ya janye karar da suka shigar gaban kotun
  • Tun farko dai Amaechi ya bukaci a soke zaben fidda gwani na jam'iyyar ADC wanda ya bai wa Atiku tikitin takarar shugaban kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya shigar yana kalubalantar zaben fitar da gwanin ADC.

Amaechi ya kalubalanci nasarar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC a zaben 2027.

Amaechi.
Dan takarar mataimakin shugaban kasa na ADC, Rotimi Amaechi Hoto: Chubuike Rotimi Amaechi
Source: Facebook

The Nation ta ce mai shari'a Joyce Abdulmalik ta yanke hukuncin ne bayan lauyan Amaechi, Jibrin Okutepa (SAN), ya sanar da kotun cewa bangarorin sun sasanta rikicin da ke tsakaninsu, tare da gabatar da bukatar janye karar.

Kara karanta wannan

'Tana da kishin addini': An shiga jimami bayan rasuwar mahaifiyar Amaechi

Kotu ta amince da janye karar

Lauyan Smaechi ya roki kotun da ta yi watsi da karar, kuma mai shari'a ta amince da bukatar nan take.

Tun farko, Amaechi ya bukaci kotun ta soke zaben fidda gwani na shugaban kasa da ADC ta gudanar a ranar 25 ga Mayu, 2026, yana mai cewa an karya tanade-tanaden Dokar Zabe ta 2026 da kundin tsarin mulkin jam'iyyar.

Amaechi ya kalubalanci nasarar Atiku

A cikin karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1215/2026, Amaechi ya shigar da Atiku Abubakar, ADC da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) a matsayin wadanda ake kara.

Ya bukaci kotun ta soke takarar Atiku, ta hana shi gabatar da kansa a matsayin dan takarar shugaban kasa na ADC a zaben 2027, tare da hana INEC amincewa da shi.

Haka kuma ya bukaci a umarci jam'iyyar ta sake gudanar da sabon zaben fidda gwani cikin kwanaki 14 bisa tanadin doka.

Ba a yi amfani da rajistar mambobi ba

Kara karanta wannan

PFIPC: Gbajabiamila ya gagara hakuri, ya maka Adeyemi a kotu, ya bukaci diyyar N10bn

Ya kalubalanci sakamakon da jam'iyyar ta sanar a ranar 27 ga Mayu, inda Atiku ya samu kuri'u 1,846,370, Amaechi ya samu 504,177, yayin da Mohammed Hayatu-Deen ya samu kuri'u 177,120.

A cewarsa, ba a yi amfani da rajistar mambobin jam'iyyar wajen tantance masu kada kuri'a ba kamar yadda doka ta tanada.

Atiku da Amaechi.
Dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakr da mataimakinsa, Rotimi Amaechi a wata ganawa da suka yi a Abuja Hoto: @atiku
Source: Twitter

Ya kuma yi zargin cewa takardar sanar da sakamakon zaben ba ta dauke da sa hannu, kwanan wata ko sunayen mambobin kwamitin zabe da wakilansa.

Sai dai bayan bangarorin sun cimma matsaya ta sasanci, kotun ta yi watsi da karar tare da kawo karshen shari'ar, kamar yadda Leadership ta kawo.

Ana son raba Atiku d Amaechi

Kun ji cewa wata kungiyar siyasa ta bukaci Atiku Abubakar ya sauya tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi a matsayin mataimakinsa.

Kungiyar ta ce Amaechi ba shi da karfin siyasa da zai kara wa ADC damar samun kuri'u a babban zaben 2027 mai zuwa.

Ta gargadi tsohon mataimakin shugaban kasa , Atiku Abubakar, da kada ya tafi da tsohon gwamnan Jihar Rivers din a matsayin mataimakinsa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262