Rigimar Takara tsakanin Mutanen Gwamnonin APC da Shugabannin Jam'iyya Ta Tafi Kotu
- Sauya sunayen masu son takara da aka yi a wasu jihohi ya jawo ‘yan APC sun yi karar jam’iyyarsu a wata kotun tarayya
- Alkali I. E. Ekwo ya ba da umarnin cewa jam'iyyar APC da INEC su dakata da duk wani sauyi da aka bukaci APC ta canza 'yan takara
- Kotun tarayya ta ce a ci gaba da mutunta matsayin da ake kai a halin yanzu har sai an kammala shari'a da APC da hukumar zabe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Masu neman takara a APC da ke da goyon bayan gwamnoninsu, sun fara shari’a da jam’iyyar a kotuna dabam-dabam.
‘Yan bangaren gwamnoni irinsu Hyacinth Alia da Lucky Aiyedatiwa sun kai karar shugabannin jam’iyyar APC na kasa a kotun tarayya.

Source: Facebook
The Guardian ta rahoto cewa masu burin samun takarar sun yi karar APC da hukumar INEC, suna kalubalantar zaben tsaida gwani.
Hakan ta faru ne saboda ba su yi nasarar samun tikitin tsaya wa takara a zaben 2027 ba sakamakon sauya sunayen wasu mutane 26.
Mutane bakwai masu neman takarar sanata da 18 da ke harin kujerar majalisar wakilan tarayya wannan sauyi ya shafa a jam'iyyar APC.
Shugabannin APC na kasa sun canza sunayen ‘yan takara a jihohin Kogi, Abia, Benue, Taraba, Ondo, Niger, Kwara, Kaduna da Ebonyi.
'Ya 'yan jam'iyyar APC sun nufi kotun tarayya
Masu neman samun takarar sun shigar da kara mai lamba FHC/ABJ/CS/1429/2026 a gaban I. E. Ekwo, suna rokon a ba su tutocin APC.
Wadanda suka shigar da karar sun bukaci kotu ta yi umarni INEC ta fasa karbar canjin ‘yan takara har sai an gama sauraron shari’arsu.
Sannan suna so a matsa wa jam’iyyar APC lamba ta tura sunayen su a matsayin su ne halastattun ‘yan takarar majalisa a zabe mai zuwa.
Ana zuwa wajen shi, Mai shari’a I. E. Ekwo ya yi umarni a cigaba da zama a halin da ake ciki yanzu, a mutunta yanayin da ake tukuna.

Kara karanta wannan
Matasa sun fito farautar 'yan bindiga bayan kashe wani jagoran al'umma a jihar Katsina

Source: Getty Images
Shugabannin APC ba su ji dadin zuwa kotu ba
Idan masu karar sun yi nasara a kotu, ‘yan jam’iyyar suna ganin hakan zai iya yi wa shirye-shiryen APC tasari a babban zabe na kasa.
Shugabannin gudanarwa na APC sun zura ido domin ganin yadda shari’ar za ta kaya duk da har yanzu ba a ji an yi wata magana.
Wata majiya ta soki matakin da ‘ya ‘yan na APC suka dauka, ana ganin bai dace a tafi kotu saboda sabanin takara na cikin gida ba.
Felix Morka ya yi bayanin kokarin da ake yi na neman shawo kan rigingimun na APC kamar yadda labarin ya zo a jaridar Leadership.
Sakataren yada labaran APC na kasa ya shaida cewa magana ta yi nisa wajen ganin an lallashi wadanda ba su ji dadin rasa tikiti ba.
'Yan siyasar da suka sauya-sheka daga ADC
Wannan rahoto ya yi kokarin tattaro maku jerin ‘uan siyasa ban da Peter Obi da Rabiu Kwankwaso da suka rabu da jam’iyyar ADC mai hamayya.
Manyan 'yan siyasa kamar Kabiru Marafa, Aisha Dahiru Binani da Babachir David Lawal duk sun bar ADC bayan an fara tafiya da su a shekarar nan.
Mafi yawancinsu sun koma jam'iyyar NDC ne, amma akwai wadanda suka shiga APC da LP.
Asali: Legit.ng

