An biya ‘Yan kwangila kudi N968m ba tare da sa-hannu a Ma’aikatar tsaro ba

An biya ‘Yan kwangila kudi N968m ba tare da sa-hannu a Ma’aikatar tsaro ba

- Ma’aikatar tsaro ta bada kwangilar N960m, an fitar da kudin babu amincewar FEC

- An gargadi Jami’an Gwamnatin a kan wannan kwangila, amma su ka yi taurin-kai

- ‘Yan Majalisa sun tado maganar bayan shekaru, sun bukaci a dawo da wannan kudi

Punch ta rahoto cewa wani kwamitin majalisar tarayya sun nuna fushinsu game da kudin da aka fitar, aka biya ‘yan kwangila ba tare da an bi doka ba.

‘Yan wannan kwamiti sun gano cewa jami’an ma’aikatar tsaro na tarayya sun biya ‘yan kwangila Naira miliyan 968.8 ba tare da jami’ai sun sa hannu ba.

Wani rahoto da babban mai binciken kudi na kasa, ya fitar ne ya tona asirin wadannan jami’an.

Jaridar ta ce an fitar da kudin ne ta bayan-fage domin sayo kayan kyale-kyale da na bada kyautar lambar girma domin bikin ranar tunawa da jami’an tsaro.

KU KARANTA: Abin da ya sa Buhari ya rika cewa 'Eh', ina cewa 'A'a' - Saraki

Ofishin AuGF ya tabbatar da cewa an fitar da wadannan miliyoyi daga asusun ma’aikatar tsaron ne duk da babu sa hannun majalisar zartarwa na kasa, FEC.

Haka zalika shugabannin da ke kula da aikin ma’aikatar ba su san da labarin wannan kwagila ba, amma jami’an su ka fitar da kudin a cikin Afrilun 2013.

Shugaban kwamitin da ya yi wannan bincike, Sanata Matthew Urhoghide ya karbi jan-kunnen da ofishin AuGF ya yi wa ma’aikatar tsaro a wancan lokaci.

Duk da gargadin da aka yi wa ma’aikatan a ranar 24 ga watan Afrilu, ba su fasa bada kwangilar ba, kuma ba su iya fitowa sun kare kansu gaban kwamiti ba.

KU KARANTA: Gwamnati za ta yi dambe da matsalar tashin kudin kayan abinci

An biya ‘Yan kwangila kudi N968m ba tare da sa-hannu a Ma’aikatar tsaro ba
'Yan majalisar dattawa Hoto: www.nairaland.com
Asali: UGC

An biya ‘yan kwangilar N484,415,000.00 a 2010, an karasa biyan ragowar N484,415,000.00 a 2015, 'yan majalisa su na kokarin ganin an dawo da wannan kudi.

A yau kun ji cewa ‘Yan Sandan Duniya na Interpol sun datse shirin wasu ‘Yan damfarar Najeriya na wawurar N250m da su ka yi awon gaba da su daga Jamus.

Wadannan miyagun mutane sun yi amfani da annobar COVID-19, sun tafka mahaukaciyar sata, da sunan za su shigowa jami'an lafiya da tsummar rufe fuska.

An yi nasara jami’an tsaron sun tono asirin ‘Yan damfarar da su ka yi yunkurin damfarar jama'a.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel