Hukumar EFCC ta gabatar da shaida a shari’arta da Babachir David Lawal a Kotu
- EFCC ta kai shaidan farko a shari’ar ta Babachir David Lawal zuwa kotu
- Ana zargin tsohon sakataren gwamnatin tarayyan da laifin satar N544m
- A kan wannan zargin Babachir Lawal ya rasa kujera a gwamnatin Buhari
Punch ta ce EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, ta koma kotu da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal.
Ana zargin Injiniya Babachir David Lawal da satar miliyan 544–tare da ‘danuwansa, Hamidu David Lawal, da Sulaiman Abubakar; Apeh John Monday.
Idan za ku tuna an gabatar da su a wani babban kotun tarayya na Abuja a ranar 30 ga watan Nuwamba, 2020 bayan mutuwar Alkalin da ke sauraron karar.
Da aka yi zaman jiya (Laraba), hukumar EFCC ta kira Mohammed Babansule, babban jami’i a wani bankin Najeriya, a matsayin shaidanta na farko a shari’ar.
KU KARANTA: Ban ba Ministan shari'a cin hancin Daloli ba - Akpabio
Mohammed Babansule shi ne mai kula da asusun bankin daya daga cikin kamfanonin da ake zargi da hannun a wannan laifin satar, Josmon Technologies Ltd.
Babansule ya tabbatar wa kotu cewa Apeh John Monday shi ne ke rike da asusun wannna kamfani.
Ma’aikacin bankin ya ce an bude asusun kamfanin Josmon Technologies Ltd a bankinsu ne tun 2015, amma shi sai a 2018 ya fara aiki da kamfanin da ake tuhuma.
Shaidan da aka kawo ya gabatar da wasu hujjoji da suka hada da takardun banki, CAC, fasfon kasar wajen darektan kamfanin da kuma takardunsa na kudin gida.
KU KARANTA: An fara kyankyasa yiwuwar karbar NIN wajen yi wa mutane katin zabe
Lauyan EFCC, O.I. Uket, ya roki kotu ta karbi wadannan hujjoji, kuma ta yi hakan. Alkali ya ce zai cigaba da sauraron shari’ar a yau, ranar 21 ga watan Junairu, 2021.
Kun samu labarin yadda ‘Yan Majalisa su ka samu Dalolin kudi da sunan kwangilolin mazabu a lokacin da Goodluck Jonathan ya ke rike da kujerar shugaban kasa.
Wani shaidan da EFCC ta kira a kotu ya tona badakalar da aka yi a baya inda kamfanoni da ‘Yan Majalisa su ka rika raba ribar da aka samu daga wannan kwangiloli.
Tsohon jami'in ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya bayyana a gaban babban kotun tarayya, Abuja.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng