Tinubu Ya Kaddamar da Shirin Tallafin Rage Talauci na Dala Biliyan 3.05

Tinubu Ya Kaddamar da Shirin Tallafin Rage Talauci na Dala Biliyan 3.05

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya buɗe manyan shirye-shiryen ci gaba guda biyar da darajarsu ta kai dala biliyan 3.05
  • Shirye-shiryen sun ƙunshi NG-CARES da SOLID da kuma rukunin shirye-shiryen HOPE na bunkasa ilimi da lafiya a fadin kasa
  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa matakin zai taimaka wajen rage radadin talauci da samar da ayyuka a matakin mazabu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da gagarumin shirin tallafi da ci gaban al'umma guda biyar na dala biliyan 3.05 domin yaƙi da talauci a Najeriya.

Shugaban ya bayyana shirye-shiryen a matsayin wani babban mataki na gaggawa da zai rage talauci, ƙarfafa al'umma, da kuma haɓaka bil'adama a faɗin ƙasar.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

The Nation ta wallafa cewa shirin ya ƙunshi ƙarin tallafin kuɗi na NG-CARES, shirin tallafa wa 'yan gudun hijira na SOLID, da kuma rukunin shirin HOPE guda uku da suka shafi shugabanci, lafiya (HOPE PHC) da ilimi (HOPE Edu).

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa ta gabatar da dokar da ta shafi hana wa'azi

Bayanin ministan kudi

Rahoton the Cable ya nuna cewa ministan kuɗi, Taiwo Oyedele, ne ya wakilci shugaba Bola Tinubu a wurin taron ƙaddamarwar.

A cewarsa, an tsara waɗannan shirye-shirye ne don mayar nasarorin tattalin arziki da aka samu zuwa inganta rayuwar al'umma a matakin mazabu.

"Wannan ba taron shirye-shirye ba ne kawai; cika alƙawari ne na gwamnatinmu. Mun zo ne da nufin gyara tattalin arziki, kare ƙasa, da saka hannun jari ga mutanenmu,"

In ji shugaban.

Kudin tallafi da za a raba

Gwamnati ta bayyana cewa shirin NG-CARES zai samu ƙarin tallafin dala biliyan 1.25 daga Bankin Duniya domin tallafa wa ƙananan manoma da ƙananan masana'antu.

Shi kuwa shirin SOLID zai samu dala miliyan 300 don samar da agajin jinkai da ci gaba ga 'yan gudun hijira (IDPs) da kuma al'ummomin da suka karɓe su.

Sauran dala biliyan 1.5 kuma za su tafi ne ga rukunin shirye-shiryen HOPE domin inganta harkokin shugabanci, lafiyar matakin farko, tallafawa malamai da ilimin bai-ɗaya.

Kara karanta wannan

'Ka hakura da neman takara a 2027': Atiku ya sake shawartar Shugaba Tinubu

Haɗin gwiwar ministoci kan shirin

A cewar Ministan Kasafi da Tsara Tattalin Arziki, Atiku Bagudu, waɗannan shirye-shirye babban martani ne na haɗin gwiwa daga gwamnatoci don magance tsadar rayuwa da ƙalubalen talauci.

Haka kuma, Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya bayyana cewa shirin HOPE PHC na dala miliyan 570 zai inganta ayyukan lafiya, samar da magunguna da kayan aiki ga mutane miliyan 40.

Pate ya ƙara da cewa an riga an inganta cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko sama da 3,000, yayin da ake shirin kammala wasu guda 1,000 nan ba da jimawa ba.

A ɓangaren ilimi, Ministan Ilimi Tunji Alausa ya bayyana cewa shirin HOPE Edu zai kai ga kusan yara miliyan 30 a jihohi 36 na ƙasar da birnin tarayya Abuja.

Ministan ilimin Najeriya na jawabi.
Ministan ilimin Najeriya, Dr Tunji Alausa. Hoto: Federal ministry of Education
Source: Twitter

Tinubu zai zauna kusa da Trump

A wani labarin, kun ji cewa wakilin Najeriya na dindindin a Majalisar Ɗinkin Duniya, Ambasada Jimoh Ibrahim, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu zai zauna kusa da Shugaban Amurka Donald Trump.

Kara karanta wannan

INEC ta sanya karin kudi cikin abubuwan da take bukata kafin zaben 2027

Wannan zama zai gudana ne a taron babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) karo na 81 da za a yi a watan Satumba mai zuwa.

Ibrahim ya bayyana hakan ne ga manema labarai bayan ya gana da Shugaba Tinubu a fadar gwamnati, inda ya tabbatar da cewa shugaban na Najeriya zai kasance a sahun gaba kusa da Trump yayin muhawarar taron.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng