EFCC ta kama Shugaban Jami'ar Tarayya ta Gusau kan almundahar kwangilar N260m

EFCC ta kama Shugaban Jami'ar Tarayya ta Gusau kan almundahar kwangilar N260m

- Hukumar EFCC ta kama Shugaban Jami'ar Tarayya ta Gusau, Farfesa Magaji Garba kan zargin almundaha

- Wani dan kwangila Alh. Shehu Sambo, mai kamfanin Ministaco Nigeria Ltd ne ya yi karar shugaban jami'ar

- Shehu Sambo ya ce shugaban jami'ar ya karbi N260m daga hannunsa da sunan zai bashi kwangilar naira biliyan 3 uku

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta kama shugaban jami'ar tarayya da ke Gusau, Farfesa Magaji Garba kan zargin almundahar kwangilar N260m, The Punch ta ruwaito.

Hukumar ta tsare shi tun ranar Alhamis da ta gabata bayan amsa gayyatar da ta masa don amsa tambayoyi game da zargin amfani da ofishinsa ba yadda ya dace ba, rashawa da almundahar kwangila.

EFCC ta kama shugaban jami'ar Gusau kan almundahar kwangilar N260m
EFCC ta kama shugaban jami'ar Gusau kan almundahar kwangilar N260m. Hoto: @MobilePunch
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Dan majalisar APC ya bindige ɗan fashi da makami har lahira a Sokoto

Wata kwakwarar majiya a hukumar yaki da rashawar ta bayyana cewa a shekarar 2018, shugaban jami'ar ya karbi naira miliyan 260 ba bisa ka'ida ba daga hannun wani dan kwangila, Alh. Shehu Sambo, mai kamfanin Ministaco Nigeria Ltd., a kan cewa jami'ar zata bawa kamfaninsa kwangilar naira biliyan 3 don gina katanga.

Sai dai kwangilar ba ta samu ba hakan yasa Sambo ya yi korafi a hukumar yaki da rashawar.

Majiyar ta ce, "Har yanzu masu bincike suna yi wa shugaban jami'ar tambayoyi domin suna son sanin abinda ya faru da kudin."

KU KARANTA: Yanzu yanzu: 'Yan PDP sun yi arangama da jami'an tsaro a Ebonyi

Mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren, a ranar Litinin, ya tabbatar da kama amma shi amma bai bada cikakken bayani ba.

A wani labarin daban, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya goyi bayan Muhammadu Buhari a shekarar 2015 duk da cewa ya san 'bai san komai ba' Olagunsoye Oyinlola, tsohon gwamnan jihar Osun ya ce.

Mista Oyinlola ya yi bayanin cewa Mista Obasanjo ya yanke shawarar goyon bayan Mista Buhari ne saboda takaicin gwamnatin Goodluck Jonathan.

Duk da cewa (shi) Obasanjo ya san cewa dan takarar na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ba zai iya tabuka wani abin azo-a-gani ba, amma duk da haka ya goyi bayansa bayan wasu jiga-jigan yan Najeriya sun matsa masa lamba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel