Kwamitin Gwamnatin Tarayya ta na ta aikin lalubo kadarorin ‘haramun’ a wurare

Kwamitin Gwamnatin Tarayya ta na ta aikin lalubo kadarorin ‘haramun’ a wurare

- An fara bibiyar dukiyoyin da Kotu ta karbe daga hannun wasu mutane

- Kotu ta bada umarni cewa wadannan dukiyoyi su koma ga Gwamnati

- Wasu daga cikin masu wadannan kadarori sun rasa su ne wajen bincike

Kwamitin gwamnatin tarayya da ke aikin sallamar da kadarori da dukiyar da aka karbe a hannun marasa gaskiya ya na cigaba da gudanar da aikinsa.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar 2 ga watan Fubrairu, 2021 cewa wannan kwamiti ya ce ya na tattara dukiyoyin da gwamnati ta yi nasarar karba.

Shugaban wannan kwamiti, Dayo Apata, ya fitar da jawabi cewa su na ta yawo wuri zuwa wuri domin tabbatar da kadarorin da aka sallama wa gwamnati.

Dayo Apata ya ce su na wannan yawo ne da nufin tantance ingancin wadannan kadarori da wasu mutane da aka damka wa gwamnati ta hanyar shari’ar kotu.

KU KARANTA: Buhari ne Shugaban farko da bai tsoma mana hannu - NNPC

Apata wanda shi ne sakataren din-din-din na ma’aikatar shari’a ya ce sun kai wannan ziyara ne da kuma nufin tantance halin da wadannan dukiya su ke ciki.

Jami’in gwamnatin ya ce su na bakin kokarinsu na ganin sun kammala wannan aiki cikin watanni shida kamar yadda shugaban kasa ya sharudanta.

A cewar Apata, kwamitin na su na bukatar hadin-gwiwar ma’aikatar ayyuka da gidaje na kasa.

Jami’an ma’aikatar ayyuka da gidaje na kasa za su taimaka ne wajen yi wa kadarorin nan kudi, domin a san irin darajar da za su yi idan an sa kayan a kasuwa.

KU KARANTA: Rikicin gado ya kai yaron Gwamnan Neja da ya rasu da mamansa kotu

Kwamitin Gwamnatin Tarayya ta na ta aikin lalubo kadarorin ‘haramun’ a wurare
Ministan shari'a Malami da Buhari Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Duk wanda ya yi rashin sa’a har aka karbe dukiyar da ya mallaka ta muguwar hanya, aka sallama wa gwamnati, wannan kwamiti zai yi dawainiyar gwanjon kayan.

Dazu kun ji cewa wasu 'yan siyasa da su ka gagara kai labari a Najeriya, sun yi taron-dangi, sun shirya kafa babbar Jam’iyyar siyasa ta hadaka da za ta ba su mulki.

Sabuwar Jam’iyyar da za a kafa ta na dauke da mutane irinsu Ghali Na-Abba, Kingsley Moghalu, da Hakeem Baba-Ahmed, Precious Elekima, da Ezekiel Nya-Etok.

Sai kuma Farfesa Pat Utomi, Farfesa Remi Sonaiya, Farfesa Chidi Odinkalu da Issa Aremu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng