Kotu ta jefa direba Kurkuku kan kashe N2m da aka tura masa cikin kuskure

Kotu ta jefa direba Kurkuku kan kashe N2m da aka tura masa cikin kuskure

- Sakamakon kin mayar da kudin da aka tura akawunt dinsa, magidanci zai ci gidan kaso

- Wannan mutum na da daman daukaka kara kotu idan bai amince da hukuncin ba

- Mutane da dama sun yi tsokaci kan hukuncin idan wasu suka ce yayi tsauri da yawa

Wata kotu dake zaune a Ilori, birnin jihar Kwara, ya yankewa wani direba hukuncin shekaru biyu a gidan kaso kan amfani da kudin da ba nashi ba.

Direban, mai suna Adetunji Tunde Oluwasegun, ya yi amfani da kudi milyan biyu da wata mata Sherrifat Omolara Sanni ta tura asusun bakinsa na GTB cikin kuskure.

Ofishin hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta gurfanar da shi a kotun ranar Litinin, 18 ga Junairu, 2021.

EFCC ta gurfanar da direban gaban Alkali Sikiru Oyinloye na babban kotun jihar Kwara kan laifin sata.

A cewarsa, laifin ya saba dokar sashe na 286 da 287 na PenalCode.

Alkali Sikiru Oyinloye ya kama direban da laifin aikata sata kuma ya yanke masa hukuncin shekaru biyu a gidan kaso tare da biyan kudin tara N200,000 (Dubu dari buyu), EFCC ta bayyana.

Bugu da kari, kotu ta umurci direban ya mayarwa matar da kudin milyan biyu cikin shekaru biyun da zai yi a gidan yari.

KU DUBA: Za mu fara yiwa duk mai son shiga Kano gwajin Korona, Ganduje

Kotu ta jefa direba Kurkuku kan kashe N2m da aka tura masa cikin kure
Kotu ta jefa direba Kurkuku kan kashe N2m da aka tura masa cikin kure Hotuna: @OfficialEFCC
Asali: Twitter

KU KARANTA: Majalisar NEC ta yi zama, ta amince a shirya maganin COVID-19 a gida

A bangare guda, ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa akan Naira miliyan dari tara (N900,000,000) gwamnatin tarayya ta bayar da kwangilar samar da shafin yanar gizo domin sayen tikitin jirgin kasa.

Amaechi ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin bikin kaddamar da shafin wanda zai koma hannun hukumar kula da jiragen kasa bayan shekara goma.

A cewar ministan, an damka kula da gudanar da shafin yanar gizon a hannun wani kamfani kafin daga bisani ya mayar da shafin hannun hukumar NRC.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng