Gaskiya Ta Fito kan Hoton da Messi ke Yi wa Yamal Wanka a Baho
- Hukumar UNICEF ta tabbatar da cewa hotunan Lionel Messi da jariri Lamine Yamal na gaske ne ba na jabu ba
- Ta ce an ɗauki hotunan ne fiye da shekaru 18 da suka gabata yayin wani taron tara kuɗaɗen tallafi na hukumar
- A halin yanzu Messi da Yamal za su fafata a wasan ƙarshe na gasar kofin duniya tsakanin Argentina da Spain
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Hukumar Kula da Yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ta tabbatar da sahihancin hotunan da ke yawo a shafukan sada zumunta, waɗanda ke nuna shahararrun 'yan wasan ƙwallon ƙafa, Messi da Yamal.
Wannan tabbaci ya kawo ƙarshen ce-ce-ku-ce da jita-jitar da aka yi ta yi na kwanaki cewa an sarrafa hotunan ne ta hanyar amfani da na'ura mai ƙwaƙwalwa.

Source: Facebook
UNICEF ta fitar da wannan bayani ne a shafinta na Facebook a ranar Alhamis, bayan da mutane da dama suka fara tantama tare da da'awar cewa hotunan na jabu ne.
Asalin hoton Messi da Yamal
A cewar hukumar, an ɗauki hotunan ne fiye da shekaru 18 da suka gabata a lokacin wani taron ɗaukar hoto don tara kuɗin tallafi na UNICEF, inda Messi ya haɗu da jariri Yamal da mahaifiyarsa Sheila.
Hukumar ta rubuta cewa:
"Kwarai kuwa, waɗancan hotunan da kuka gani na gaske ne. Fiye da shekaru 18 da suka gabata, jariri mai suna Lamine Yamal da mahaifiyarsa Sheila sun haɗu da Lionel Messi."
UNICEF ta ƙara da cewa a yau duka 'yan wasan biyu babban abin alfahari ne, kuma suna amfani da muryoyinsu a matsayin jakadun UNICEF don kare haƙƙin yara a duniya.
Yahoo Sports ta ce hukumar ta yaba wa fitaccen mai ɗaukar hoto na ƙasar Spain, Joan Monfort, wanda shi ne ya ɗauki waɗannan tsofaffin hotuna masu cike da tarihi.

Kara karanta wannan
An kai hari gidan fitaccen ɗan kwallo bayan Sifaniya ta doke Faransa a Kofin Duniya

Source: Getty Images
Yadda aka dauki hoton
Hotunan, waɗanda suka sake karbuwa sosai a kwanakin nan, sun nuna matashin Messi yana yi wa jariri Yamal wanka a cikin wani baho lokacin ana tsara kalandar tallafin UNICEF.
Hotunan sun sake bayyana ne bayan bajinta da daukakar da Yamal ya samu a duniya, inda magoya baya da dama suka kasa gaskata cewa tauraron na Barcelona ya taɓa haɗuwa da Messi tun yana jariri.
A yanzu, duka 'yan wasan biyu suna hidima a matsayin jakadun UNICEF na musamman don tallafa wa rayuwa da ci gaban yara a fadin duniya.
Messi da Yamal za su fuskanci juna a wasan ƙarshe na gasar cin kofin duniya ta FIFA da ke gudana a Amurka tsakanin Argentina da Spain a ranar Lahadi.
Argentina ta doke Ingila
A wani labarin, mun rahoto cewa ɗan wasa Lautaro Martinez ya zura ƙwallo a minti na 92 don taimaka wa Argentina doke Ingila da ci 2-1 a wasan kusa da na ƙarshe na cin kofin duniya na 2026.

Kara karanta wannan
Gwamna ya zakulo samari da zawarawa 300, zai masu auren gata da sadakin N250000 a Kebbi
Ingila ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Anthony Gordon a minti na 10 da dawowa hutun rabin lokaci na wasan da aka buga a birnin Atlanta na ƙasar Amurka.
Sai dai, Messi ya taimaka wa Enzo Fernandez ya zura ƙwallo a minti na 85, kafin Martinez ya zura wata a daidai lokacin da wasan ke daf da karewa.
Asali: Legit.ng
