Kwangilolin mazabu: "Kamfanoni da ‘Yan Majalisa su ke raba ribar da aka samu"

Kwangilolin mazabu: "Kamfanoni da ‘Yan Majalisa su ke raba ribar da aka samu"

- Wani tsohon jami’in gwamnati ya fallasa badakalar da ke cikin kwangilolin mazabu

- Mohammed Muazu ya ce kamfanoni da ‘yan majalisa su kan raba kudin da aka samu

- Wannan mutumi ya bayyana haka ne yayin da ake shari’ar Tanimu Turaki da EFCC

Wani tsohon darekta a ma’aikatar gwamnatin tarayya, Mohammed Muazu, ya bayyana rawar da ya taka wajen aikin kwangilolin mazabu da ake ba ‘yan majalisa.

Da yake magana a ranar Litinin, Mohammed Muazu ya bayyana yadda shi da wasu ‘yan majalisar tarayya suka raba ribar da aka samu daga wadannan ayyyuka a 2014.

Jaridar Premium Times ta fitar da rahoto cewa Alhaji Mohammed Muazu ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya bayyana a gaban babban kotun tarayya da ke Abuja.

Da yake magana a kotu, Mohammed Muazu, bai bada sunayen ‘yan majalisar tarayyar da su kayi kudi daga kwangilar mazabun ba, amma yace shi ya dawo da miliyoyi.

KU KARANTA: Turaki ya bar hannun EFCC bayan sa'o'i kadan a tsare

Muazu ya ce ma’aikatar ayyuka na musamman wanda Tanimu Turaki ya ke jagoranta a wancan lokaci ta shiga yarjejeniya da ‘yan majalisa domin su samu kudin kamfe.

A cewar Muazu, ana amfani da ribar da kamfanonin da aka zaba, aka ba aikin kwangilar mazabun ‘yan majalisar suka samu wajen yakin neman zabe a wancan lokaci.

Alhaji Muazu ya ce ana yin kashe-mu-raba ne tsakanin ‘yan majalisar tarayya da kamfanonin da su ka yi masu wadannan kwangilolin a mazabun da su ke wakilta.

Da Lauyan EFCC, U Ringim ya taso shaidan a gaba, ya bayyana cewa ‘yan majalisa suna zaben kamfanin da za su yi masu aiki, daga baya sai a raba kudin da aka samu.

KU KARANTA: Akpabio: Minista yana barazanar zuwa Kotu kan zargin cin hanci

Kwangilolin mazabu: "Kamfanoni da ‘Yan Majalisa su ke raba ribar da aka samu"
Ana shari'a da Kabiru Tanimu Turaki a kotu Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Tahir Haruna wanda yanzu ya mutu shi ne ya nuna wa jami’in dawar-garin. Idan an samu riba, wani mai canjin kudi ya kan canza kudin zuwa Daloli, a ba ‘yan majalisar.

Yanzu haka hukumar EFCC ta na zargin tsohon Ministan ayyuka na musamman na kasa, Tanimu Turaki SAN, da laifuffuka 16, wadanda su ka hada da satar kudi.

Tsohon jami’in gwamnatin shi ne mutum na bakwai da hukumar EFCC ta kira domin ya bada shaida a shari’ar da ake yi tsakanin hukumar da Tanimu Turaki.

A halin yanzu dai gwamnatin tarayya ta kammala shirin ruguza hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC da takwararta ICPC, za a kafa wata sabuwar hukuma.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel