Yadda Turaki ya karkatar da kudin Gwamnati a asusun jama’a inji Jami’in EFCC
- Shaidu su na cigaba da bayyana a shari’ar EFCC da Kabiru Tanimu Turaki
- Wani jami’in EFCC ya ce sun gano N75m a asusun matar tsohon Ministan
- An aikawa mai dakinsa wasu kudi da aka ware da za a wayar da kan jama'a
Jami’in hukumar EFCC, Bello Hamma-Adama, ya shaida wa Alkalin babban kotun tarayya na Abuja, Inyang Ekwo, sun karbe kudi daga hannun Halima Turaki.
Jaridar Punch ta rahoto cewa Halima Turaki, matar tsohon Ministan Najeriya, Kabiru Tanimu Turaki ce.
Dr. Kabiru Tanimu Turaki ya rike kujerar Ministan harkoki na musamman da sha’anin gwamnati a lokacin mulkin Dr Goodluck Jonathan tsakanin 2013 da 2015.
Kabiru Tanimu Turaki wanda ya nemi takarar shugaba kasa a 2015 ya taba rike Ministan kwadago, kuma ya na cikin jagoroin jam'iyyar PDP a fadin Najeriya.
KU KARANTA: EFCC ta yi ram da tsohon Minista, Turaki
Hamma-Adama shi ne shaida na biyar da ya yi magana a shari’ar da ake yi da Tanimu Turaki da hadiminsa Sampson Okpetu, wadanda EFCC ta ke zargi da cin kudi.
Wannan shaida da lauyan EFCC, Mohammed Abubakar, ya kawo ya bayyana gaban Alkali mai shari’a Inyang Ekwo, ya ce an wawuri N359m daga ma’aikatar Turaki.
Hamma-Adama ya ce bayan an zari wadannan kudi da sunan wayar da kan al’umma, an karkatar da su ga asusun kanin Ministan da mai dakinsa da wani mutum.
Da aka yi bincike an gano N45m a asusun kanin Ministan, Abdullahi Maigwandu, wanda karamin ma’aikacin gwamnatin jiha ne da albashinsa N30, 000 ne a wata.
KU KARANTA: Sabuwar annoba ta bayyana a Sokoto, ta kashe mutane 4 - Gwamna
Maigwandu ya ce ya tura N20m daga cikin wannan kudi zuwa asusun Halima Tanimu Turaki.
Jami’in na EFCC ya fada wa Alkali cewa bayan nan, an aika wa wani Abubakar Sani Gude N30m, a karshe wannan kudi ya kare a asusun mai dakin tsohon Ministan.
A zaman da aka yi na karshe a kotu, wani tsohon jami’in gwamnati ya fallasa badakalar da ke cikin kwangilolin mazabu a lokacin da Turaki ya ke kujerar Minista.
Tsohon ma'aikacin da aka kira ya bada shaida a kotu, ya ce kamfanoni da kuma ‘yan majalisa su kan raba kudin da aka samu daga kwangilolin mazabu da ake bada wa.
Alkali Inyang Ekwo ya ce za a cigaba da sauraron shari'ar a ranar 9 ga watan Fubrairu, 2011.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng