Ana Shirin Cafke Tinubu idan Ya Je Amurka? Jakadan Najeriya Ya Yi Bayani
- Jakadan Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Ambasada Jimoh Ibrahim, ya yi magana kan shirin cafke Bola Tinubu
- Jimoh ya ce jita-jitar da ake yadawa cewa Bola Tinubu zai fuskanci kama a Amurka karya ce, babu hujjar doka
- Sanata Jimoh Ibrahim ya tabbatar Tinubu zai halarci taron Majalisar Dinkin Duniya, ya gabatar da jawabi kan tsaron duniya, sannan ya dawo Najeriya lafiya ba tare da matsala ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Jakadan dindindin na Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Ambasada Jimoh Ibrahim, ya yi magana kan jita-jitar da ake yadawa.
Jimoh Ibrahim ya musanta rade-radin cewa Shugaba Bola Tinubu na fuskantar barazanar kama idan ya je Amurka.

Source: Facebook
Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels Television ranar Alhamis.
An karyata rahoton shirin cafke Tinubu
Jimoh Ibrahim ya bayyana wannan ikirari a matsayin karya, yana mai cewa babu wata hujjar doka da za ta sa a kama shugaban Najeriya.
Jakadan ya ce Shugaba Tinubu zai halarci taron Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya, wato UNGA, ba tare da wata matsala ba sannan zai dawo Najeriya lafiya.
Ya ce masu hasashen cewa za a kama shugaban suna yada jita-jita marasa tushe, yana tambayar irin laifin da shugaban ya aikata.
A cewarsa, idan Tinubu ya halarci taron kuma ya dawo lafiya, mutane za su fahimci cewa shugaban Najeriya ya cancanci girmamawa daga kowa.
Jimoh Ibrahim ya kuma bayyana cewa an ware wa Tinubu kujera ta uku ko ta hudu a sahun gaba a wajen zaman Majalisar Dinkin Duniya.
Ya ce tsarin zaman ya riga ya kammala, kuma babu wanda zai iya canza wannan tsari ko hana shugaban halartar taron.
Jakadan ya kara da cewa Tinubu zai gabatar da muhimmin takarda kan tsaron duniya tare da shiga tattaunawar da ta shafi sauye-sauyen Majalisar Dinkin Duniya.
Har ila yau, ya bukaci 'yan Najeriya su kara amincewa da shugabanninsu da cibiyoyinsu maimakon yada maganganu marasa tushe.
Jimoh Ibrahim ya tuna cewa lokacin da aka nada shi jakadan Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya, wasu sun yi ikirarin ba zai iya shiga Amurka ba.
Sai dai ya ce Majalisar Dinkin Duniya ta amince da shi, an zabe shi zuwa wani muhimmin matsayi, kuma yanzu yana jagorantar kwamitin kasafi da gudanarwa mai kula da kasafin kusan dala biliyan 18.5.
Ya kuma ce ya taba karatu a Jami'ar Harvard, yana mai jaddada cewa ikirarin cewa ba zai iya shiga Amurka ba ma karya ce.
A karshe, ya bukaci 'yan Najeriya su daina raina shugabanninsu da cibiyoyinsu, su rika ba su goyon baya da girmamawa.
Tinubu ya shirya rage talauci a Najeriya
Mun ba ku labarin cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya buɗe manyan shirye-shiryen ci gaba guda biyar da darajarsu ta kai dala biliyan 3.05.
Shirye-shiryen sun ƙunshi NG-CARES da SOLID da kuma rukunin shirye-shiryen HOPE na bunkasa ilimi da lafiya a fadin kasa.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa matakin zai taimaka wajen rage radadin talauci da samar da ayyuka a matakin mazabu.
Asali: Legit.ng

