Jam'iyyar APC
Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe ya sanar da cewa APC za ta yi zaben fitar da gwani na ƙato bayan ƙato idan har masu neman takara ba su yarda da sulhu ba.
Gwamnatin Kebbi ta zargi tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, da munafuncin siyasa bayan bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna karkashin jam’iyyar ADC.
Mai neman takarar gwamnan jihar Gombe karkashin inuwar jam'iyyar APC, Farfesa Isa Ali Pantami, ya yi gargadi ga jam'iyya mai mulki kan zaben 2027.
Ƙungiyar TMG ta soki kalaman Isa Ali Pantami kan zaben 2027, tana gargadin cewa irin wadannan furuci na iya haddasa tashin hankali da barazana ga dimokuradiyya.
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya yi magana kan gudanar da zaben fitar da gwani. Ya bayyana cewa a shirye APC ta ke ta gudanar da zaben fitar da gwani na gwamna.
Sanata mai wakiltar Gombe ta Kudu, Anthony Siyako, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP mai adawa. Sanatan ya koma PDP ne bayan rasa tikitin jam'iyyar APC.
Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, bai halarci tantancewar APC ba yayin da jam’iyyar ta tantance gwamnoni 14 da sauran masu neman mukaman zaben 2027.
Mutum 6 daga cikin wadanda suka nuna sha'awar takarar gwamnan jihar Yobe a Inuwar APC sun garzaya sun gana da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.
A labarin nan, za a ji cewa duk da rigingimun shugabanci da ya dabaibaye wani sashe na APC, jam'iyyar tana cinikin fam har ta tara sama da N4bn gabanin 2027.
Jam'iyyar APC
Samu kari