Ana Rade Radin Sakataren ADC na Kasa Ya Koma APC, Aregbe Ya Yi Magana
- Sakataren jam'iyyar ADC na kasa, Rauf Aregbesola ya yi magana kan rade-radin da aka fara cewa yan komawa tafiyar APC mai mulki
- Rauf Aregbesola ya yi martani kan jita-jitar ne a wani taron jam'iyyar ADC da aka gudanar a Osun, inda ya nuna cewa za su yi nasara a 2027
- Aregbesola ya yi gwamna a Osun, ya kuma rike ministan a karkashin jam'iyyar APC a lokacin Muhammadu Buhari amma ya koma ADC
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Osun - Sakataren jam’iyyar ADC, Rauf Aregbesola ya sake jaddada biyayyarsa ga jam’iyyar tare da yin watsi da jita-jitar cewa ya koma tsohuwar jam’iyyarsa ta APC.
An yada jita-jitar cewa ya koma APC ne yayin da ake cigaba da tantance 'yan takara domin tunkarar babban zaben 2027 a Najeriya.

Source: Facebook
Legit Hausa ta gano cewa Rauf Aregbesola ya yi martani ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook bayan taron jam'iyyar a Osun.
Sakataren ADC bai koma APC ba
Tsohon gwamnan jihar Osun ya bayyana cewa yana ADC ne a Ilesa da ke jihar Osun ranar Lahadi yayin taron shugabanni da masu ruwa da tsaki da ya samu halartar mahalarta daga gundumomi 332 na jihar.
A wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran ADC a Osun, Oluwaseun Abosede ya sanya wa hannu, an ce Aregbesola ya kuma gabatar da ɗan takarar gwamnan jam’iyyar a zaɓen Osun na ranar 15 ga Agustan 2025, Najeem Salaam.
Da yake ci gaba da jawabi a taron, Aregbesola ya bayyana zargin cewa ya koma APC a matsayin:
“Maras tushe kuma abin dariya,”
Punch ta rahoto ya kara da cewa Arebe ya yi magana yana mai cewa tun bayan ficewarsa daga APC fiye da shekara uku da suka gabata bai taɓa samun wani dalilin komawa cikinta ba.
Ya ƙara da cewa:
“APC ta yi watsi gaba ɗaya da manufofinta na asali da kuma akidun da suka shafi jin daɗin jama’a waɗanda ya kamata gwamnati ta tsaya a kansu.
"Babban manufar gwamnati ita ce walwalar jama'a da tsaro, amma an yi watsi da su an kuma jefar da su cikin kwandon shara.”
Arebe ya ce yana jam'iyyar ADC
Aregbesola ya sake tabbatar da biyayyarsa ga ADC, yana mai cewa duk da yunƙurin da wasu masu ƙarfin faɗa a ji ke yi na hana jam’iyyar ci gaba, tana ci gaba da bunƙasa tare da samun manyan nasarori.
Ya buƙaci mambobi da masu ruwa da tsaki na ADC da su koma gundumominsu domin ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a a matakin ƙasa domin shirye-shiryen ayyukan da ke gaba.

Source: Facebook
Ya kuma yi hasashen cewa ADC za ta samu nasara a zaɓen shekarar 2027 tare da kira ga mambobi da su ƙara jajircewa wajen tallafa wa manufofin jam’iyyar.

Kara karanta wannan
Tsohon shugaban kasa, Jonathan ya canza jam'iyya don ya fito takara a 2027? Gaskiya ta bayyana
Nafiu Bala ya gargadi 'yan ADC
A wani labarin, kun ji cewa tsagin jam'iyyar ADC da Nafiu Bala ke jagoranta ya yi gargadi ga David Mark da ya dakatar da sayar da fom din neman takara.
Bangaren Nafiu Bala ya bayyana cewa yana so a dakatar da sayar da fom din har sai kotu ta yanke hukunci a kan karar da ya riga ya shigar.
A yanzu haka dai manyan 'yan siyasa da suka hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya saye fom din neman takara a zaben 2027.
Asali: Legit.ng

