Sanata Hanga Ya Yi Tone Tone kan Dalilin Rabuwarsa da Kwankwaso

Sanata Hanga Ya Yi Tone Tone kan Dalilin Rabuwarsa da Kwankwaso

  • Rufai Hanga ya bayyana abin da ya jawo rashin jituwa tsakaninsa da madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
  • Sanatan ya zargi Kwankwaso da nuna rashin jin daɗi kan yadda ayyukan tallafinsa suka ƙara masa farin jini a tsakanin jama’a
  • Hanga ya ce rashin jituwa da “Jagora” ya taka rawa wajen hana shi samun tikitin sake tsayawa takara a jam'iyyar NDC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kanao - Sanatan da ke wakiltar Kano ta Tsakiya, Rufai Sani Hanga, ya yi magana kan dalilinsa na raba gari da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Sanata Hanga ya bayyana cewa rashin jituwarsa da Kwankwaso, ta samo asali ne daga sabani kan ayyukan tallafa wa jama’a da harkokin siyasa.

Sanata Hanga ya raba gari da Kwankwaso
Sanata Rufai Hanga tare da Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Rigimar ta fara ne kan shirin tallafa wa jama’a

Sanata Rufai Hanga ya bayyana hakan ne yayin wata hira da tashar talabijin ta yanar gizo, Dan’uwa Rano TV.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: An bayyana wadda ta yi silar hadakar Kwankwaso da Peter Obi

Ya ce Kwankwaso ya fara nuna rashin jin daɗi da shi bayan ya shirya babban shirin tallafa wa mazabarsa.

Sanatan ya ce a lokacin shirin, ya raba motoci, shinkafa, taki, injinan nika da sauran kayan tallafi ga al’ummar Kano ta Tsakiya.

Kwankwaso ya fusata da taron rabon kaya

Hanga ya ce rashin jituwar ta ƙara tsananta ne bayan ya gudanar da rabon kayan a wani wuri da ke da alaƙa da Kwankwaso.

A cewarsa, Kwankwaso ya amince zai halarci taron domin shaida rabon kayan, amma lokacin da ya isa wurin ya nuna rashin jin daɗi.

Ya ce an tara motoci, buhunan shinkafa, taki, dabbobi da sauran kayan tallafi a wurin, waɗanda aka kwashe kusan kwana ɗaya da rabi ana jigilar su zuwa wurin taron.

Hanga ya ce Kwankwaso ya bukaci a dakata domin a yi sallah, sannan ya bar wurin amma bai dawo ba.

Sai dai rabon kayan ya ci gaba a gaban wasu fitattun ‘yan siyasa, ciki har da tsohon Mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, Wada Sagagi, Batayya, Nasiru Gawuna da wasu ‘yan Majalisar Tarayya.

Kara karanta wannan

Da gaske hukumar Hisbah ta hana Kiristoci gudanar da ibada a Sokoto

Hanga ya bayyana abin da Kwankwaso ya gaya masa

Sanatan ya ce daga baya Kwankwaso ya yi masa magana kan taron, yana zarginsa da gudanar da rabon kayan ne domin jama’a su rika yabonsa saboda abin da yake yi a Kano ta Tsakiya.

Hanga ya ambato Kwankwaso yana cewa bai kawo kayan tallafin wurinsa domin a raba su ba, duk da cewa ya ba shi buhunan shinkafa da taki da kuma shanu.

Sanatan ya ce ya ba Kwankwaso haƙuri tare da alkawarin warware duk wata rashin fahimta da ta samu tsakaninsu.

“Jagora bai ji daɗin ayyukana ba”

Hanga ya ce abin da ya faru ya sa ya fahimci cewa girmamawar da ke tsakaninsa da Kwankwaso ta fara raguwa.

Ya ce Kwankwaso bai ji daɗin yawan ayyukan tallafinsa da rabon kayan da yake yi ba, musamman yadda hakan ke ƙara masa farin jini a tsakanin jama’a.

Sanatan ya danganta rashin samun tikitin sake tsayawa takara da tabarbarewar dangantakarsa da Kwankwaso, wanda ya kira “Jagora” na tafiyar Kwankwasiyya.

Kara karanta wannan

Matar aure ta biyewa zuciya ta kona diyar mijinta da ruwan zafi

“Dalilin da ya sa ban samu tikiti ba shi ne ‘Jagora’ Kwankwaso bai ji daɗin ayyukana da harkokina ba,” in ji Hanga.

An yi ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun Kwankwaso, Saifullahi Hassan, da kuma mai magana da yawun tafiyar Kwankwasiyya, Dr Habibu Sale Mohammed, amma ba a samu amsar kira ko saƙonnin da aka aika musu ba.

Hanga ya yi magana kan Kwankwaso
Sanata Rufai Hanga na jawabi a wajen taro Hoto: Rufai Sani Hanga
Source: Facebook

Sanata Hanga ya bar NDC

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanatan da ke wakiltar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, Rufai Hanga, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar NDC.

Ya bayyana cewa ya bar jam'iyyar ne domin ya mayar da hankali kan wasu harkokinsa da kuma manufofinsa na kashin kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng