Biyu Babu: An Rasa Sunan Tsohon Shugaban Yan Sanda cikin Yan Takarar Gwamna
- Hukumar INEC ta fitar da sunayen ’yan takarar gwamnan a fadin Najeriya baki daya yayyin da ake shirin zabe
- Daraktan yaƙin neman zaɓen Mohammed Adamu ya ce tsohon IGP ya koma SDP bayan ya fice daga APC mai mulki
- Ya ce Adamu yana cikin takarar gwamna kuma suna da takardun da ke tabbatar da rajistarsa, duk da cewa INEC ta sanya wani suna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta fitar da jerin sunayen ’yan takarar kujerar gwamnan Nasarawa, amma sunan Mohammed Abubakar Adamu bai bayyana ba.
Mohammed Abubakar Adamu, tsohon Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, ba ya cikin jerin sunayen da hukumar ta wallafa na ’yan takarar zaɓen gwamnan.

Source: Facebook
INEC ta fitar da sunayen yan takara
INEC ta fitar da sunayen ’yan takarar da jam’iyyunsu, waɗanda hukumar ta amince da su domin shiga takarar kujerar gwamnan Nasarawa, cewar Premium Times.
A cikin jerin sunayen akwai Ahmed Aliyu Wadada na jam’iyyar APC; Musa Adamu Angbazo na SDP; Dahiru Musa Doma na APP; da Jonathan Gaza Gbefwi na LP.
Sauran ’yan takarar sun haɗa da Retired Major General Nuhu Angbazo na ADC; Emmanuel David Ombugadu na PDP; da Ibrahim Kasimu Aboh na APGA.
Haka kuma, akwai Christopher Mamman na ADP; Abdullahi Omame Abisabo na PRP; Abubakar Abdu Giza na ZLP; Mohammed Awwal Suleiman na APM; da Abdullah Bukhari na AA.
Kigbu John Tanko na YPP; Dogo Danladi Shammah na NDC; da Shuaibu Umaru Kubi na Accord su ne sauran ’yan takarar da aka bayyana.

Source: Original
Tsohon IGP ya yi rijista da SDP
Sai dai Daraktan Yaɗa Labarai na Ƙungiyar Yaƙin Neman Zaɓen tsohon IGP, Abdullahi Yammani, ya tabbatar da cewa Adamu ya yi rajista da SDP.
Yammani ya ce tsohon IGP ya kammala rajistarsa tda SDP bayan ya yi murabus daga APC, inda ya sha kaye a zaɓen fidda gwani.
Ya ce an yanke shawarar ne bayan tuntubar masu ruwa da tsaki a kananan hukumomi 13 na jihar, tare da cewa Adamu zai yi amfani da ƙwarewarsa wajen tsaro da mulki.
Yammani ya ce tsohon shugaban ’yan sandan zai yi amfani da kwarewarsa wajen magance matsalolin da ke addabar Nasarawa idan ya samu nasara a zaɓen.
Wannan tabbaci ya zo ne yayin da sunan Adamu ya ɓace daga jerin INEC, wadda a halin yanzu ta sanya Musa Adamu Angbazo a matsayin ɗan takarar SDP.
Sai dai Yammani ya nuna kyakkyawan fata cewa za a warware matsalar, yana cewa ƙungiyar kamfen na da dukkan takardun da ke tabbatar da rajistar Adamu.
Ya ce takardun sun kuma tabbatar da takararsa a ƙarƙashin jam’iyyar SDP, duk da cewa sunansa bai bayyana cikin jerin INEC da aka wallafa ba.
Martanin APC bayan rasa tsohon IGP
Mun ba ku labarin cewa jam’iyyar APC a Nasarawa ta yi martani bayan ficewar tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Mohammed Abubakar Adamu.
Shugaban APC na jihar, Aliyu Bello, ya buƙaci magoya bayan Adamu su amince da sakamakon zaɓen fitar da gwani, yana mai cewa iko daga Allah yake.
Bello ya ce kona tsintsinya ba zai lalata tasirin APC ba, yana mai yabawa ayyukan gwamnati da ci gaban da aka samu a jihar.
Asali: Legit.ng

