Takara: Kalaman Pantami Sun Tayar da Kura, an Shawarce Shi kan Zaman Lafiya
- Wata kungiya a Najeriya ta soki kalaman da aka danganta da Farfesa Isa Ali Pantami kan zaben fitar da gwani na APC a Gombe
- Ƙungiyar ta yi gargadin cewa irin wadannan furuci na iya haddasa tashin hankali da barazana ga dimokuradiyya
- Ta ce dole ne a gudanar da zabubbuka cikin gaskiya da lumana, ba tare da amfani da barazana, tsoratarwa ko tayar da rikicin siyasa ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Kungiyar sa ido kan mulki ta 'Transition Monitoring Group' ta yi Allah wadai da kalaman da ake dangantawa da tsohon ministan sadarwa, Isa Ali Pantami.
Kungiyar ta bayyana damuwa game da kalamansa da yi kan zaben fitar da gwani da aka yi a jihar Gombe game da zaben 2027.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Auwal Musa Rafsanjani, ya sanya wa hannu, cewar The Nation.
Kungiya ta ja hankalin Pantami kan siyasa
Kungiyar ta bayyana kalaman a matsayin masu tayar da hankali da hadari ga dimokuradiyya inda ta ja hankalin Farfesan da ya kula yayin maganganunsa domin tabbatar da zaman lafiya.
TMG ta ce furucin da ke nuna adawa da sakamakon zabe idan bai yi wa wasu dadi ba, zai iya rage yarda da hukumomin dimokuradiyya.
Kungiyar ta ce tana Allah wadai da duk wani furuci da zai iya jawo rikicin zabe, tsoratarwa ko tada fitina kafin babban zaben shekarar 2027.
Ta jaddada cewa dole ne a yanke hukuncin zabubbuka ta hanyar gaskiya da adalci, ba tare da amfani da barazana, karfi ko cin zarafi ba.
TMG ta kuma yi tir da kashe-kashen da ake dangantawa da rikicin siyasa, tana gargadin ‘yan siyasa su guji kara dagula yanayin kasar nan.

Source: Twitter
An shawarci yan siyasa kan zaman lafiya
Kungiyar ta nuna damuwa kan yadda siyasa ke kara zama ta kudi da magudi, musamman a zaben fidda gwani na jam’iyyun siyasa daban-daban, cewar Premium Times.
Ta bukaci shugabannin addini su yi amfani da mukamansu wajen yada zaman lafiya, hadin kai da kyawawan dabi’un dimokuradiyya a tsakanin jama’a.
TMG ta kuma bukaci ‘yan Najeriya su yi rajistar zabe, su karbi katin zabe na dindindin, sannan su shiga zabukan 2027 cikin lumana da kwanciyar hankali.
Kungiyar ta yi kira ga jam’iyyun siyasa, ‘yan takara, hukumomin tsaro, kotuna da hukumar zabe ta INEC su tabbatar da adalci da bin doka.
A karshe, TMG ta gargadi masu ruwa da tsaki kan amfani da kalaman kiyayya, rarrabuwar kabila da addini, daba da kuma anfani da hukumomin gwamnati domin muradun siyasa.
Legit hausa ta yi magana da masoyin Pantami
Wani mazaunin cikin kwaryar Gombe kuma masoyin Farfesa Pantami ya yi tsokaci kan maganganu da ake yi game da kalaman malam.
Muhammad Adamu ya ce mutane suna juya kalamansa ko kuma ba su fahimci abin da yake nufi ba.
Ya ce:
"Malam cewa ya yi fa zai yaki zalunci da rashin adalci kuma ta hanyar doka saboda shi mutum ne mai ilimi ba zai yi abin da zai kawo rigima a kasa ba."
Tikitin takara: Gwamna Inuwa ya magantu
An ji cewa Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya ya bayyan cewa kowane dan siyasa ya san iya karfinsa, saboda haka za a yi zaben fitar da gwani.
Ya bayyana haka ne bayan tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Pantami ya ki amincewa da sulhu a APC.
Fitaccen malamin wanda ya nuna sha'awar tsaya wa takarar gwamna ya ce ba zai amince da abin da ya kira zalunci a neman mulki ba.
Asali: Legit.ng


